An Zo Wurin: Gwamnatin Tinubu Za Ta Lafta Harajin Fetur kan Yan Najeriya bisa Sharadi 1

An Zo Wurin: Gwamnatin Tinubu Za Ta Lafta Harajin Fetur kan Yan Najeriya bisa Sharadi 1

  • Gwamnatin tarayya za ta fara karɓar harajin mai bayan tattalin arziki ya daidaita, kuma kuɗaɗen shiga na ’yan Najeriya sun inganta
  • Ministan Kudi, Taiwo Oyedele Ya ce kuɗaɗen da za a samu daga harajin za a yi amfani da su wajen gina tituna da samar da tanadin mai
  • Oyedele ya bayyana cewa gwamnati ba za ta fara karɓar harajin a ɓoye ba, domin sai an fitar da sanarwa a hukumance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigerian - Ministan kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin Najeriya, Taiwo Oyedele, ya ce gwamnatin tarayya za ta sanya haraji a man fetur idan yan Najeriya suka samu wadata.

Oyedele ya ce gwamnati za ta kirkiro wannan haraji ne idan tattalin arzikin ƙasar ya daidaita, sannan kuɗaɗen shiga na ’yan Najeriya sun inganta har za su iya ɗaukar nauyin harajin.

Kara karanta wannan

'Farashin abinci ya zube kasa warwas a Najeriya saboda tsare tsaren Tinubu'

Taiwo Oyedele.
Ministan Kudi kuma Mai Tattalin Arzikin Najeriya, Taiwo Oyedele Hoto: Taiwo Oyedele
Source: Twitter

Oyedele ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da wakilin sashen kasuwanci na Arise TV, Rotus Odiri, a gefen taron shekara-shekara na asusun ba da lamuni na duniya (IMF) da Bankin Duniya na shekarar 2026.

Gwamnatin tarayya za ta sa harajin fetur

Da aka tambaye shi ko gwamnati na shirin ƙirkiro da harajin mai, Oyedele ya ce wasu kasashe na karbar haraji tsakanin kashi 20 zuwa 80 cikin 100 na farashin mai.

Ya ce ƙaddamar da harajin mai a lokacin da ake ci gaba da tallafa wa farashin man fetur zai zama kamar aikin banza, domin gwamnati ce za ta biya harajin a zahiri.

Ministan ya ƙara da cewa sanya harajin nan take bayan cire tallafin man fetur zai ƙara wa ’yan Najeriya nauyin tsadar rayuwa..

“Nan gaba a lokacin da ya dace, bayan tattalin arziki ya daidaita kuma kuɗaɗen shigar yan Najeriyanya kai matsayin da zai iya ɗaukar nauyin harajin, za a fara karɓar waɗannan haraje-haraje. Ba wai don muna son ɗora haraji ba ne.”

Kara karanta wannan

Shirin gwamnatin Tinubu bayan wa'adin rangwamen farashin fetur ya ƙare

Harajin mai zai tallafa wa tituna

Ministan ya ce za a ware kuɗaɗen da aka samu daga harajin domin gina da inganta tituna, da kuma samar da tanadin man fetur domin taimakawa wajen daidaita farashin kayayyakin mai idan wani abu ya faru.

Oyedele ya ƙara da cewa tanadin zai kuma iya zama wata hanya ta rage tasirin tashin farashi, ta yadda gwamnati za ta iya dakatar da karɓar harajin na ɗan lokaci idan farashin mai ya fuskanci wani tashin gwauron zabi a nan gaba.

Tinubu.
Mai zuba fetur a gidan mai da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a gefen dama Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A rahoton The Cable, Ministan ya ce:

“Abu mai kyau shi ne, doka ta tanadi cewa ba za a fara aiwatar da harajin ba sai an fitar da sanarwa a hukumance.
"Dole ne ministan kuɗi ya fitar da umarni a hukumance, wanda ke nufin ba za mu iya yin hakan a ɓoye ba. Bugu da ƙari, ba mu da niyyar yin wani abu a ɓoye.”
“A lokacin da ya dace, kowa zai fahimci dalilin da ya sa ake buƙatar kakaba harajin fetur, kuma kowane ɗan Najeriya zai fahimci amfaninsa.”

Kara karanta wannan

Akwai dalili: Me yasa gwamnoni 33 ke goyon bayan tazarcen Tinibu?

Gwamnatin tarayya za ta saukaka rayuwa

Kun ji cewa Gwamnatin tarayya na aiki tukuru don rage hauhawar farashi zuwa ƙasa da 10%, in ji mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga.

Onanuga ya bayyana hakan ne yayin sanar da wasu ƙarin matakan da gwamnati ta ɗauka domin tallafa wa ’yan Najeriya a daidai lokacin da ake fuskantar matsalar farashin mai a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262