Tinubu Ya Nada Jega Da AbdulAziz Matsayin Masu Magana Da Yawunsa

Tinubu Ya Nada Jega Da AbdulAziz Matsayin Masu Magana Da Yawunsa

  • Tinubu ya nada shahrarrun yan jarida daga Arewa biyu matsayin sabbin masu magana da yawunsa
  • Mahmud Jega da Abdulaziz Abdulaziz sun samu shiga cikin jerinsu Festus Keyamo da sauransu
  • Tinubu ya ce ya nada su saboda su bada tagomashi wajen kamfensa a yankin arewacin Najeriya

Abuja - Dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 mai wakiltar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, ya nada Mahmud Jega matsayin mai bashi shawara kan harkokin jama'a.

Hakazalika Tinubu ya nada Abdulaziz Abdulaziz matsayin mataimakin mai magana da yawunsa, rahoton Leadership.

Tinubu
Tinubu Ya Nada Jega Da AbdulAziz Matsayin Masu Magana Da Yawunsa
Asali: Twitter

Tunde Rahman, mai magana da yawun Tinubu ya bayyana hakan a jawabin da yayi satin nan, yace wadanda aka nadan zasu yi amfani da tunaninsu da kwarewarsu akan abinda ya shafi siyasa a fadin kasar nan musamman ma arewacin kasar wurin bunkasa ayyukan da ya shafi kafafen sadarwa.

Kara karanta wannan

'Dan Takarar Gwamna a 2023 Ya Yi Alƙawarin Kafa Gwamnati Bisa Koyi da Annabi Muhammad SAW

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tunde yace:

"Jega babban edita ne kuma mai sharhi a tashar Arise TV kuma yana yiwa jaridar Thisday rubutu mako-mako. Hakazalika ya kasance Cif Editan jaridar 21st Century Chronicle."
"Jega a baya ya kasance Malamin Aji a tsangayar ilmin halitta a jami'ar Usmanu Danfodio dake Sokoto, sannan ya bazama aikin jarida na tsawon shekaru 30."
"Abdulaziz kuwa shahrarren dan jarida ne kuma mataimakin edita a jaridar Daily Trust."
"Tsawon shekaru 13 ya kasance manaja edita, mataimakin edita kuma shugaban jaridar DailyTrust. Gabanin haka ya rike mukamin edita a jaridar New Nigerian Newspapers, edita a mujallar Sentinel, kuma mataimakin edita a mujallar Citizen."
"Ya yi aiki matsayin wakilin jaridar Leadership kuma ya rike mataimakin edita a jaridar Blueprint da ya bari a 2017."

Yan Takarar Shugaban Kasa na Neman Samun Goyan Baya Da Kuma Kuri'un Yan Arewa Maso Gabas

Kara karanta wannan

Tinubu ya fi Shettima Lafiya, Rawar 'Buga' Da Yayi Alama ce, 'Dan Majalisar Wakilai Dambazau

Masu takarar kujerar shugaban kasa a Nigeria a zaben 2023 suna matukar bukatar neman kuri'ar yan arewa maso yamma a Nigeria.

Yan siyasan su bazama yankin domin samun kuri'un wannan yanki.

Yankin na da yawan kuri'u kusan miliyan 22.2. Jihohin da ke yankin sun hada da Katsina, Kaduna, Kano, Zamfara, Sokoto, Kebbi, da Jigawa.

Yankin dai wanda shine a gaba wajen yawan wanda suke da rijista kada kuri'a a Nigeria.

Asali: Legit.ng

Online view pixel