Ana Maganar Shiga APC, Abba Kabir Ya Caccaki Ganduje, Ya Yabi Kwankwaso
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya raba kayayyakin tallafi ga matasa 2,260 da suka kammala shirin koyon sana’o’i guda takwas
- Abba Kabir Yusuf ya ce an assasa cibiyoyin ne a zamanin Rabiu Musa Kwankwaso amma aka rufe su a gwamnatin Abdullahi Ganduje
- Ya jaddada kudurin gwamnatinsa na farfaɗo da shirye-shiryen matasa a yayin da ake maganar zai sauya sheƙa a siyasa zuwa APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar dawo da martabar shirye-shiryen tallafa wa matasa, tare da yaba wa irin tubalin da gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso ta assasa a baya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin rabon kayayyakin tallafin dogaro da kai ga matasa 2,260 da suka kammala karatu daga cibiyoyin koyon sana’o’i guda takwas a faɗin jihar Kano.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da gwamman ya yi a taron ne a wani sako da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature D-Tofa ya wallafa a Facebook.
Abba ya rabawa matasan Kano 2,260 tallafi
An gudanar da bikin rabon kayayyakin tallafin ga matasa 2,260 a ranar Lahadi, 11, Janairu, 2026, a filin Open Arena da ke Gidan Gwamnati, Kano.
A cewar sanarwar da gwamnatin Kano ta fitar, ta ce shirin na daga cikin matakan da ta ke dauka domin ƙara samar da ayyukan yi ga matasa.
Abba Kabir Yusuf ya ce manufar shirin ita ce sake farfaɗo koyar da sana'o'i da ba matasa dama, da buɗe ƙofofin basirarsu domin su zama masu dogaro da kai da kuma masu bayar da gudummawa ga tattalin arzikin jihar.
Gwamna Abba ya yabi gwamnatin Kwankwaso
Gwamnan ya tunatar da jama’a cewa cibiyoyin koyon sana’o’in da aka farfaɗo da su an kafa su ne a zamanin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, domin bai wa matasa ƙwarewar aiki da za su dogara da kansu.

Kara karanta wannan
"Bai yi butulci ba": Kwamishina a Kano ya wanke Abba daga zargin juya wa Kwankwaso baya
A cewarsa, dawo da cibiyoyin da kuma bai wa masu kammala karatu kayan aiki da jarin fara kasuwanci zai taimaka wajen rage rashin aikin yi da kuma bunƙasa tattalin arzikin Kano.
Abba Gida Gida ya yi wa Ganduje gugar zana
Abba ya zargi gwamnatin da ta gabata ƙarƙashin Abdullahi Ganduje da yin sakaci da shirye-shiryen matasa, yana mai cewa hakan ya janyo cikas ga dubban matasa masu sha’awar koyon sana’a.
Ya bayyana takaicinsa kan yadda gwamnatin Ganduje ta rufe cibiyoyin, lamarin da ya janyo tsaiko ga ci gaban matasa da dama a jihar Kano.
A rabon tallafin, daliban sun samu kwamfutoci da kayan gyaran waya, daliban kiwon dabbobi, kaji da kifi sun samu kwai, keji, abinci da magunguna da sauransu.

Source: Facebook
Ganduje ya dawo Najeriya daga Dubai
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya dawo Najeriya bayan shafe kwanaki a Dubai.
Abdullahi Ganduje ya dawo Najeriya ne a daidai lokacin da ake rade-radin gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf zai shiga jam'iyyar APC.
Wasu rahotanni sun nuna cewa Ganduje zai fara tattauna wa da manyan 'yan siyasa a kan sauya shekar gwamnan da ake magana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
