Suswam: Tsohon Gwamna Ya Musanta Satar Dukiyar Jama'a, Ya Fadi Inda Ya Samu Kudinsa

Suswam: Tsohon Gwamna Ya Musanta Satar Dukiyar Jama'a, Ya Fadi Inda Ya Samu Kudinsa

  • Tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam, na fuskantar tuhumar yin sama da fadi da kudin gwamnati lokacin da yake kan mulki
  • Gabriel Suswam ya bayyana cewa bai taba wawushe kudin gwamnati ba lokacin da yake kan mulki daga shekarar 2007 zuwa 2015
  • Tsohon Sanatan ya nuna cewa duk da abin da ake biyansa bai da yawa, yana da wasu hanyoyin da yake samun kudin rike iyalinsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Benue - Tsohon gwamnan jihar Benue, Sanata Gabriel Suswam, ya kare kansa a gaban kotu kan zargin satar kudaden gwamnati.

Gabriel Suswam ya bayyana a gaban kotu cewa bai taba satar kudi gwamnati ba a lokacin da yake gwamna daga shekarar 2007 zuwa 2015.

Gabriel Suswam ya musanta satar kudaden gwamnati
Gabriel Suswam na jawabi a wajen wani taro Hoto: Gabriel Suswam
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Gabriel Suswam ya gabatar da wannan jawabi ne a ranar Laraba, 22 ga watan Oktoban 2025 a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fadi abin da yasa ya gagari mayu da masu kambun baka

Tsohon sanatan ya yi bayanin ne yayin da yake kare kansa kan tuhumar EFCC da ke zarginsa da karbar haramtattun kudade, tare da tsohon kwamishinan kudi na jihar, Omadachi Okolobia.

Ina Suswam yake samun kudi?

“Ina da gonar shinkafa da kiwon shanu, ba kudin gwamnati nake amfani da su ba”

- Gabriel Suswam

Suswam ya bayyana cewa duk da cewa albashinsa na gwamna bai wuce N700,000 ba, yana samun karin kudin shiga ta hanyar noman shinkafa da kuma kiwon shanu, wanda kundin tsarin mulki ya amince wa shugabanni masu rike da mukamai su yi.

"Ofishin gwamna yana da girma a suna, amma kudin da ake biya 'yan kadan ne."

- Gabriel Suswam

Suswam ya kare kansa a kotu

Tsohon gwamnan ya musanta cewa ya taba karbar wasu kudade da ake zargin cewa kason jihar Benue daga kamfanin Benue Cement Company (BCC).

Ana zargin cewa wani mai canjin kudi, Abubakar Umar, ya kai masa Dala miliyan 15.8 (kimanin naira biliyan 3.1) a gidan gwamnatin Benue da ke Maitama, Abuja.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Lokacin da aka yi yunkurin kifar da gwamnatin Obasanjo a mulkin farar hula

Tun da farko Abubakar Umar ya bada shaidar cewa ya kai kudin zuwa wani gida mallakin gwamnatin Benue da ke Maitama, Abuja.

Suswam ya kare kansa gaban kotu
Tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam Hoto: Gabriel Suswam
Source: Facebook
“Na san Abubakar Umar, amma a wannan batu, ban taba yin wata mu’amala da shi ba dangane da abin da ake tuhuma."
"Ban taba ba shi umarni ya karbi kudi, ya canja su sannan ya dawo min da su ba kamar yadda ake zargi ba. Ban taba yin irin wannan mu’amala da shi ba."

- Gabriel Suswam

Alkalin kotun mai shari’a Peter Lifu ya dage sauraron karar zuwa ranakun 5 da 12 ga watan Nuwamban 2025 domin ci gaba da shari’a.

Sanata Suswam ya ragargaji Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam, ya yi kalaman suka kan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Gabriel Suswam ya bayyana cewa shugaban kasan bai yi kokari ba wajen rage wahalhalun da 'yan Najeriya suke fuskanta.

Tsohon gwamnan ya ce Shugaba Tinubu bai ɗauki matakan rage raɗaɗin wahalhalun da manufofin gwamnatin jam’iyyar APC suka haifar ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng