Gwamna Ya Amince a Kashe N1bn a Fannoni 3, za a Sayo Littattafan N588m a Jihar Katsina
- Majalisar zartarwa ta Katsina ta amince da kashe fiye da Naira biliyan daya don ayyuka a fannonin lafiya, ilimi da kuma makamashi
- Gwamna Dikko Radda ya halarci taron majalisar na 10 ta yanar gizo yayin da aka yanke shawara kan ayyukam da za su amfani jihar
- An ware fiye da Naira miliyan 588 don sayen littattafai, Naira miliyan 500 don abinci mai gina jiki da kuma kudin sayo gidan sauro
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Majalisar zartarwar jihar Katsina ta amince da kashe fiye da Naira biliyan daya domin aiwatar da sababbin ayyuka a bangarorin lafiya, wutar lantarki da kuma ilimi.
Wannan na cikin kudirin Gwamna Mallam Dikko Umaru Radda na samar da ci gaba mai dorewa a Katsina karkashin tsarin "Gina Makomarka."

Asali: Facebook
An yanke shawarar ne a yayin taron majalisar zartarwa karo na 10 da aka gudanar ranar Talata, wanda Mataimakin Gwamna Faruk Lawal Jobe ya jagoranta, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rahoto cewa Gwamna Dikko Radda ya halarci taron ne ta hanyar kiran bidiyo, domin tabbatar da ci gaba da gudanar da mulki ba tare da tangarda ba.
Kudin da Katsina ta warewa fannin lafiya
A cikin wata ganawa da manema labarai bayan kammala taron, wasu manyan jami’an gwamnati da suka hada da kwamishinan yada labarai, Dr. Bala Salisu Zango, kwamishinan lafiya Dr. Musa Adamu, da Mai bai wa gwamna shawara kan ilimin firamare da sakandare, Nura Saleh, sun bayyana muhimman ayyukan da aka amince da su.
Yayin da yake bayani kan bangaren lafiya, Dr. Musa Adamu ya bayyana cewa majalisar ta amince da Naira miliyan 500 a matsayin kaso na jihar domin samun irin wannan adadin daga asusun UNICEF don fadada shirin ciyar da yara abinci mai gina jiki a fadin jihar.
A wani bangare na taron, majalisar ta amince da shiga cikin wani shiri na yaki da zazzabin cizon sauro, tare da hadin gwiwar Kungiyar lafiyar iyali (SfF) da kuma Global Fund.
Jihar za ta bayar da kashi 30 na dukkanin kudaden da ake bukata, yayin da kungiyar SfF da gidauniyar GF za su dauki nauyin ragowar kaso 70 din.
Haka kuma, The Nation ta rahoto cewa majalisar ta amince da sayen gidajen sauro guda 400,000 domin cike gibin da ke akwai na kashi 30 a fadin jihar.
Gwamnati ta ware kudin sayen babban janareta
A bangaren wutar lantarki, kwamishinan watsa labarai, Dr. Bala Salisu Zango ya ce majalisar ta amince a sayo janareta mai karfin megawat 1, a wani yunkuri na ingata samar da wutar lantarki a jihar.
Dr. Bala Zango ya kuma ce nan gaba kadan aiki zai kankama na samar da sabon tsarin samar da wutar lantarki da zai tallafawa manoman rani da sauran ayyukan noma a jihar.
Ya ce duk wutar lantarkin da aka samar mai yawa za ta rika bi ta hannun KEDCO wanda hakan zai taimaka wajen rarraba wuta a sassan jihar.

Asali: Twitter
Za a raba littattafan N588m a Katsina
Mai bai wa gwamna shawara kan ilimin firamare da sakandare, Nura Saleh, ya sanar da cewa majalisar ta amince da kashe Naira miliyan 588 domin saye da raba littattafai 156,566 zuwa makarantun sakandare 578 a fadin jihar.
Littattafan da za a saya sun hada da na darasin lissafi, Ingilishi, Physics, Chemistry, Biology, Basic Science, Civic Education.
Sauran littattafan da gwamnatin ke son rabawa daliban jihar sun hada da koyon adabi a Ingilishi, Economics, Hausa da kuma ilimin addinin Musulunci.
Gwamnan Katsina shi ne mafi aiki a 2025
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya lashe lambar yabo ta gwamnan da ya kowane gwamna aiki a 2025.
Aso Multimedia ce ta ba gwamnan wannan lambar yabo domin yabawa kokarin da yake wajen kawo ci gaba da fannoni daban-daban a Katsina.
Kwamishinar harkokin mata ta Katsina, Hajiya Hadiza Yar’adua ta faɗi wasu daga cikin ayyukan da Dikko Ummar Raɗɗa ya yi a shekaru biyu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng