'Ba Tsoro ba ne': Gwamnan Sokoto Ya Bayyana Dalilin Yin Sulhu da 'Yan Bindiga
- Gwamnatin Sokoto ta bayyana sulhu da ƴan bindiga da suka miƙa wuya a matsayin dabarar magance ta'addancin da ke faruwa a jihar
- Mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan tsaro, Kanar Ahmed Usman (rtd), ya ce dabara ce ta tsaro ta sa suka nemi sulhu ba tsoro ba
- Gwamnati ta ce za ta ci gaba da amfani da ƙarfin bindiga ga 'yan ta'adda a inda ya kamata, amma ta buɗe ƙofar sulhu ga masu mika wuya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Gwamnatin Sokoto ta kare matakin da ta dauka na yin sulhu da ƴan bindiga waɗanda suka miƙa wuya da kansu a jihar.
Gwamnatin ta bayyana yin sulhu da ƴan bindigar a matsayin wata babbar hanya mai ɗorewa ta kawo ƙarshen hare-hare a sassan jihar.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce bayanin gwamnatin martani ne ga kalaman wani mai sharhi a kafofin sada zumunta, Basharu Altine Giyawa, wanda ya soki lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Ba mu yi sulhu don tsoro ba' - Gwamnatin Sokoto
Mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan harkokin tsaro, Kanar Ahmed Usman (mai ritaya), ya ce gwamnatin Sokoto ba ta yin sulhu da ƴan bindigar don tana jin tsoron su ba.
Kanar Ahmed ya shaida cewa:
"Akwai bukatar a fayyace gaskiya game da dalilin Gwamna Ahmed Aliyu na ɗaukar dabarun tsaro daban-daban da suka haɗa da yin sulhu da ƴan bindigar da suka tuba.
"Abin mamaki ne da takaici yadda Basharu Giyawa ya canja alkibla a yanzu, alhali shi ne da kansa ya taɓa nuna aniyarsa ta shiga tsakani tsakanin jihar da waɗanda 'yan bindiga.
"Maganar gaskiya ita ce, gwamnati ba ta yin sulhun nan saboda tana jin tsoro ba. Abin da muke yi shi ne rungumar tsarin da ya dace, samar da tsaro ba dole sai da bakin bindiga ba."

Kara karanta wannan
'Ƴan bautar ƙasa sun fi mu albashi': Lakcarori a babbar makaranta sun koka a Kaduna
Manufar gwamnati da martani ga masu suka
Kanar Ahmed Usman ya ce dole ne a rika tunawa da mazauna Rabah, Goronyo, Isa, Sabon Birni da sauran ƙananan hukumomin da ke rayuwa cikin fargabar hare-hare a kullum.

Source: Facebook
Ya ce rashin tsaro ya sa manoma sun bar gonakinsu, wanda ya sa samar da abinci ya ragu, kuma ayyukan samar da tattalin arziki sun tsaya cak a yawancin garuruwan.
"Manufar mu a bayyane take: dawo da zaman lafiya, dawo da mutanenmu zuwa gidajensu, da kuma sake gina tattalin arzikin jiharmu.
"Wannan ba nuna gazawa ba ce, wannan sulhu ne na dabarun samar da zaman lafiya da ci gaban al'umma na dogon lokaci."
- Kanar Ahmed Usman
Gwamnati ta yi kira ga masu sukar matakinta da su kasance masu yin magana bisa adalci da gaskiya, tana mai cewa:
"Kalubalen da jihar Sokoto ke fuskanta na buƙatar haɗin kai, ba rarrabuwar kawuna ba; haɗin gwiwa, ba zargi ba. Gwamna Ahmed Aliyu na aiki tuƙuru don samarwa al'umma mafita."
'Yan bindiga suna da alkawari?
A zantawarmu da wani mai sharhi kan lamuran tsaro, Nura Haruna, ya ce abin tambayar kullum shi ne, 'Yan bindiga suna da alkawari?'
A cewar Nura Haruna:
"Mun ga yadda aka yi zaman sulhu da 'yan bindiga a jihohi da dama, amma a karshe me ya faru? Sun koma sun sake daukar makamai suna farmakar mutane.
"A duk lokacin da aka ce gwamnatin jiha ko kuma mazauna wani gari sun yi zaman sulhu da 'yan bindiga, to tambayar ita ce, su wadannan 'yan bindigar suna da alkawari?
"Idan ka duba jihar Katsina, an yi zaman sulhu da 'yan bindiga a sassa da dama, amma me ya hakan ya haifar? Kusan kowanne mako sai ka ji inda suka kai hari.
"A zamfara ma, an yi sulhu da 'yan bindiga, a Sokoto ma an yi suhu da 'yan bindiga, amma duka me ya haifar? Hakan bai hana an ci gaba da kashe mutane ba."
Nura ya yi kira ga gwamnatocin jiha da tarayya da su yi mai yiwuwa wajen dawo da zaman lafiya a Najeriya da kuma hana kashe-kashen da 'yan bindiga ke yi.
An bude kofar sulhu da 'yan bindiga a Sokoto
Tun da fari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Sokoto ta bayyana aniyarta ta magance matsalar rashin tsaro ta hanyar sulhu da tattaunawa da ‘yan bindigar da suka tuba.
Ta bayyana cewa za a yi sulhu ne kawai da ‘yan bindigar da suka ajiye makami, kuma suka yi alkawarin yin zaman lafiya da al'umomin jihar.
Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), mai ba gwamna shawara kan tsaro, ya ce an samu nasarar dakile kashe-kashe da dama a baya ta hanyar irin wannan sulhu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


