An Shiga Tashin Hankali a Kaduna, Mutum 8 Ƴan Gida 1 Sun Mutu a Hanyar Zaria
- Mummunan hatsarin mota a hanyar Kaduna ya yi sanadiyar mutuwar mutum takwas 'yan gida ɗaya, ciki har da mai juna biyu
- Wata mota kirar Mercedes GLK Jeep da wani yaro ke tukawa ce ta buge su yayin da suke tsaye a bakin hanya, sannan ya tsere
- Iyalan waɗanda abin ya shafa sun koka kan rashin tausayi daga gwamnati da kuma iyalan direban da ya haddasa wannan hatsarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna – Wani mummunan haɗarin mota da ya faru da yammacin Litinin a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria ya yi sanadiyyar mutuwar mutum takwas 'yan gida daya.
Daga cikin wadanda suka rasa ransu akwai mace mai juna biyu (tagwaye), yayin da wasu biyu ke kwance a asibiti ana kokarin ceton rayukansu.

Kara karanta wannan
Da gaske sojoji sun hamɓarar da shugaban ƙasa a Kamaru? Bincike ya bankaɗo gaskiya

Source: Facebook
Hatsarin mota ya kashe mutum 8 a Kaduna
An ce hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 6:00 na yamma a yankin Barakallahu, yayin da iyalan suka fito daga gidan kakarsu domin murnar babbar Sallah, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa wata mota kirar Mercedes GLK mai launin toka, da wani yaro dan unguwar Rigachikun ke tukawa ce ta kwace, ta turmushe mutanen.
An ce 'yan gida dayan na tsaye ne a bakin hanya suna jiran motar haya lokacin da direban Marsandin, wanda ake zargin ɗan wani babban ɗan siyasa ne, ya buge su, kuma ya tsere daga wurin.
“Na rasa matata, ‘ya’ya biyu da ‘yan uwa” – Mai Yadi
Malam Jamilu Usman Mai Yadi, wanda ke zaune a Sabon Gari, Tudun Wada, ya bayyana yadda ya rasa matarsa, Khadija Umar, da ‘ya’yansa biyu – Sadiq mai shekaru 16 da Muhammad mai shekaru tara a haɗarin.
Malam Jamilu ya shaida wa manema labarai cewa:
“Na rasa mutum takwas daga cikin iyalina. Ciki har da ‘yan uwanta mata biyu da wata yayarsu. Mutum 10 motar ta buge, takwas sun mutu, biyu kuma suna kwance a asibiti."
Mai Yadi ya ce sun tsaya ne a bakin hanya suna jiran abin hawa, ba tare da sanin cewa motar da za ta kawo ƙarshen rayuwarsu na dab da isowa ba.
“Kafar matata ta yi raga-raga. Har sai daga bisani ne jami'an hukumar kiyaye hadurra suka kawo gawar ɗana Sadiq."
- Malam Jamilu Usman Mai Yadi.
“Matata na dauke da juna biyu tagwaye” – Mai Shinkafa
Daya daga cikin mamatan, Zainab Muhammad, na dauke da juna biyu tagwaye. Mijinta, Malam Sulaiman Mai Shinkafa, ya ce matarsa ta rasu 'yan kwanaki kafin lokacin haihuwarta.
“Mun shirya komai, har sunan tagwayen muka saka: Hassan da Hussaini. Hadarin ya kuma rutsa da danmu Khalid, mai shekara 6," inji Mai Shinkafa cikin hawaye.
Ya kara da cewa gawar Zainab ta yi rugu-rugu, kuma kasusuwan ɗansu sun tarwatse a kan hanyar, sakamakon bangar da motar ta yi masu.
Yayin da yake magana yana zubar da hawaye, Mai Shinkafa ya ce:
“Dole sai da muka rika tattaro naman jikinsu, muka hade su kafin mu biene su. Wannan ya zama babban tashin hankali da ba kowa ne zai iya jure wa ba."

Source: Original
“Babu wanda ya zo mana ta’aziyya" - Mai Shinkafa
Mai Shinkafa da sauran dangin mamatan sun koka kan yadda babu wani jigo daga gwamnatin jihar Kaduna ko iyalan direban da ya haddasa haɗarin da ya zo musu gaisuwar ta’aziyya.
“Ko kalma guda babu daga gwamnati ko iyayen yaron. Mahaifin direban ma bai ko tuntube mu ba. Kamar dai rayukanmu ba su da wani amfani,” inji Mai Shinkafa.
Al’umma sun fara kira ga hukumomi da su binciko wanda ya haddasa haɗarin, tare da daukar matakin da ya dace domin ganin an samu adalci ga iyalan da abin ya shafa.
'Yan gida 1 su 8 sun mutu a hatsarin mota
A wani labarin makamancin wannan, mun ruwaito cewa, ƴan sandan Imo sun tabbatar da mutuwar mutane takwas 'yan gida ɗaya a wani mummunan hatsarin mota.
Rahoton ƴan sandan ya nuna cewa iyalan suna kan hanyarsu ta zuwa gida don bikin sabuwar shekara ne lokacin da hatsarin ya afku.
Hatsarin mai ban tsoro ya afku ne da misalin ƙarfe 3:00 na yammacin ranar Laraba, 29 ga watan Disamba, a mararrabar Amanwozuzu da ke ƙaramar hukumar Ikeduru.
Asali: Legit.ng


