Da Ɗumi-ɗumi: Haɗarin Mota Ya Laƙume Rayukan Mutane 10 A Abia
- Hadarin Mota ya jawo asarar rayukan da suka kai 10 akan babbar hanyar Aba zuwa jihar Enugu
- Wani ganau ba jiyau ba yace tayar motar ce ta fita, sai kuma motar ta fara wuntsilawa
- Motar ta haya ce cike da fasinjoji, kuma ta taso ne daga garin Aba zata je Enugu.
Mutane aƙalla 10 ne aka tabbatar da sun mutu a sakamakon mummunan haɗarin mota daya rutsa dasu akan babban titin Aba zuwa Enugu a jiya Laraba.
Wannan haɗari dai ya faru ne a Ohiyya kan titin zuwa Umuahia babban birnin jahar Abia kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.
KARANTA ANAN: Bincike ya fallasa yadda masu hakar gwal ta bayan-fage suke hura wutan rashin tsaro
Wani da lamarin ya faru a gaban shi ya shaida ma manema labarai cewa haɗarin ya faru ne sakamakon fashewar tayar baya ta motar.
KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: An Bayyana ranar da za'a yima shugaba Buhari Da Osibanjo allurar rigakafi
Faruwar hakan keda wuya sai motar tayi ta wuntsila-wuntsila inda daga bisani kuma ta kama da wuta.
Yace motar ta haya ce wacce ta taso daga garin Aba zata je garin Enugu a yayin da wannan mummunan lamari ya faru.
A wani labarin kuma Gwamnoni zasu tattauna kan yadda za'a raba rigakafin corona
Gwamnonin kasar nan zasu shiga tattaunawa da junansu a kan yadda za'a gudanar da allurar rigakafin cutar corona
Babban makasudin taron shine yadda za'a rarraba kashin farko na rigakafin kamar yadda me magana da yawun kungiyar ya sanar
Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.
Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd
Asali: Legit.ng