Hatsarin Kwale-Kwale: Mutum 16 Yan Gida Daya Sun Mutu a Jihar Neja

Hatsarin Kwale-Kwale: Mutum 16 Yan Gida Daya Sun Mutu a Jihar Neja

  • An sake samo gawarwakin manoma shida cikin wadanda suka rasu a hatsarin kwale-kwale a yankin Mokwa ta jihar Neja
  • An rahoto cewa mutum 16 cikin wadanda suka rasu a hatsarin yan gida daya ne domin dai suna da alaka ta jini
  • Al'ummar yankin sun roki gwamnati da ta kawo masu dauki domin dai hanyar ruwa ne babban hanyar sufuri da suke da shi a yankin

Jihar Neja - Rahotanni sun kawo cewa an tsamo karin gawarwakin manoma shida da suka rasa rayukansu a hatsarin kwale-kwale da ya afku a garin Gbajibo dake karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja.

Legit.ng ta rahoto cewa a safiyar ranar Lahadi, 10 ga watan Satumba ne mutum 24 suka rasu a hatsarin yayin da har yanzu ba a ga wasu ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hawaye Sun Zuba Yayin Da Kwale-Kwale Ya Sake Ajalin Mutane Da Dama Bayan Ya Kife A Cikin Ruwa

Yan gida daya 16 sun mutu a hatsarin kwale-kwale
Hatsarin Kwale-Kwale: Mutum 16 Yan Gida Daya Sun Mutu a Jihar Neja Hoto: @Daily_Trust
Asali: Twitter

Yan gida daya 16 sun kwanta dama a hatsarin kwale-kwale

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mutum 16 daga cikin wadanda suka rasu a hatsarin yan gida daya ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata cikin dangin da abun ya shafa mai suna Hajiya Kashi Mokwa, ta fada ma jaridar Daily Trust cewa cikin mamatan akwai diyarta, jikoki da sauran yan uwansu.

Hajiya Kashi ta ce:

“Muna cikin bakin ciki da abun da ya faru. Rasa yan uwa 16 babban bala’i ne kuma ya faru da mu. Suna a hanyarsu ta zuwa gona ne lokacin da jirgin ya yi karo da kututture a karkashin ruwa.
"Saboda yawan ruwan ya karu a yanzu sakamakon yawan ruwan sama da ake yi, ba za ka ga wadannan kututturen ba.
"Muna so gwamnati ta kawo mana dauki. Hatsarin kwale-kwale ya fara yawa. Ya kasance abin tashin hankali gare ni da sauran dangina. Inda kuka rasa yan uwa 16 cikin dangi a lokaci guda, ta yaya mutum zai jure wannan bala'i?

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kuma Kai Mummunan Farmaki Da Tsakar Dare, Sun Yi Ajalin Mutane 11, 'Yan Sanda Sun Yi Martani

"Idan gwamnati za ta aiko mana da kayan rage radadi, a aiko garemu kai tsaye. Mutanenmu basu da rigar ruwa. Ba gaskiya bane cewa basa son amfani da shi. Wadanda gwamnati ke ta bayarwa basu isa ba.
"Duk suna hanyar zuwa gona ne tare da yara da mata kuma ruwa ne babban hanyar sufurinmu. Ba za mu iya isa ga gonakinmu ba tare da ketare ruwan ba. Ya kamata gwamnati ta taimaka mana saboda Allah."

Kwale-kwale ya kife da fasinjoji da dama a Adamawa

A gefe guda, mun kawo a baya cewa an sake samun hatsarin jirgin ruwa a kauyen Gurin da ke karamar hukumar Fufore na jihar Adamawa.

Lamarin ya faru a ranar Litinin 11 ga watan Satumba da rana wanda mafi yawan fasinjojin mata ne da yara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel