Zamfara: Mutane 7 sun mutu a gida daya bayan sun yi kalacin rana da fate-fate

Zamfara: Mutane 7 sun mutu a gida daya bayan sun yi kalacin rana da fate-fate

Mutane bakwai ne jaridar Daily Trust ta rawaito cewa sun mutu a gida daya bayan sun yi kalacin rana da 'fate-fate' a gidansu da ke kauyen Auki a karamar hukumar Bangudu da ke jihar Zamfara.

Yahaya Abdullahi, dan uwa ga dangin mamatan, ya shaidawa Daily Trust cewa wata yarinya ce mai shekaru 12 ta dafa fate-faten da ya zama sanadin ajalinta da mutane 6 a gidansu.

"Ita da kanta yarinyar ta debo tsakin masara tare da sanar da mahaifiyarta cewa za ta dafa mu su fate-fate, ita kuma mahaifiyar ta amince.

"Daga nan sai ta nemi mahaifiyarta ta bata sauran kayan girki da suka hada da kafi zabo da sauransu.

"Ita kuma mahaifiyar aiyuka sun yi ma ta yawa, a saboda haka ba ta bawa yarinyar kayan girkin da ta bukata ba.

"Saboda haka, sai yarinyar ta shiga neman kafi zabo da kanta a dakin mahaifiyarta.

"A nan ne aka samu kuskure, yarinyar ta debo gishirin lalle bisa tunanin cewa kafi zabo ne da ake zubawa a girki.

"Kun san gishirin lalle yana matukar kama da farin kafi zabo da aka fi sani da 'A ji no motto'.

"Da gishirin lallen ta yi amfani wajen dafa fate-faten," a cewar Yahaya.

Zamfara: Mutane 7 sun mutu a gida daya bayan sun yi kalacin rana da fate-fate
Zamfara: Mutane 7 sun mutu a gida daya bayan sun yi kalacin rana da fate-fate
Asali: Twitter

Sannan ya cigaba da cewa; "bayan ta kammala abincin, ta zuba wanda za ta ci tare da kaninta, ta zubawa kannenta mata su uku, ta zubawa mahaifiyarta da kishiyar mahaifiyarta.

"Cikin sa'a daya kacal bayan sun kammala cin fate-faten, sai suka fara wata irin rashin lafiya tare da fitar da wani farin kumfa daga bakinsu.

DUBA WANNAN: Kano: Ministan Buhari ya kaddamar da wani katafaren gini da aka kammala a BUK (Hoto)

"Ita yarinyar da sauran 'yan uwanta hudu; mata uku da namiji daya, sun mutu bayan wani takaitaccen lokaci.

"Mahaifiyarta da kishiyarta sun mutu bayan an kwantar dasu a asibitin garin Bungudu.

"Yanzu haka wata yayar yarinyar da ta sha fate-faten, a lokacin da ta zo ziyara gidan, ta na shan magani a asibiti, kuma da alamun sauki a tattare da ita.

"Ita ce kadai ake saka ran za ta tsira da ranta daga cikin wadanda suka sha fate-faten," a cewarsa.

Daily Trust ta rawaito cewa Hassan Jauro, mahaifin yarinyar mai suna Maimuna, ya kidime tare da rantawa zuwa cikin daji a dimauce.

Da kyar wata tawagar jama'a su ka samu nasarar kamo shi a cikin jeji tare da mayar da shi gidansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng