Mace Mai Juna Biyu Ta Mutu Saboda Asibiti Sun Ce Sai 'Cash' a Kaduna

Mace Mai Juna Biyu Ta Mutu Saboda Asibiti Sun Ce Sai 'Cash' a Kaduna

  • Dokar sauya fasalin Naira na CBN yayi sanadiyar mutuwar wata mata mai juna biyu a jihar Kaduna
  • Mijin, ya bayyana cewa asibiti sun ki karban matarsa mai nakuda saboda ya kasa biyan tsabar kudi
  • Kotun koli za ta koma zama ranar Laraba domin cigaba da sauraron karar da aka shigar kan lamarun Naira

Kajuru LGA, jihar Kaduna - Rashin isassun tsabar kudi a Najeriya ya yi sanadiyar rashin rayuwar wata mata bayan an gaza biyan tsabar kudi a asibiti don a karbi haihuwarta.

A cewar Daily Trust, matar wacce mazauniyar Kasuwar Magani ce dake karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

An garzaya da matar asibiti tana nakuda amma haka aka mayar da ita gida saboda rashin tsabar kudi.

Naira
Mace Mai Juna Biyu Ta Mutu Saboda Asibiti Sun Ce Sai 'Cash' a Kaduna Photo credit: Benson Ibeabuchi/Bloomberg
Asali: Getty Images

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Kuna cutar da talakawa: Atiku ya caccaki CBN da Buhari kan sabuwar dokar kudi

Mijin matar, James Auta, ya bayyana cewa asibitin sun ki karbar haihuwar matarsa bayan ya gaza samun kudi daga ATM da kuma wajen yan POS.

A cewarsa, wannan abu ya faru ne a makon da ya gabata.

An tattaro cewa matar a mutu a gida bayan jini ya ki tsayawa bayan haihuwa.

Wannan labari ya tada hankulan jama'a inda su tofa albarkacin bakinsu.

Legit ta tattauna da wata Ungozoma yar jihar Kaduna, Malama Umaira Usman, inda ta yi alhinin abinda ya faru.

"A gaskiya abinda sukayi bai dace ba. Idan mace tazo haihuwa bai kamata ace saboda babu kudi suki karbi haihuwarta ba.
Idan ka duba ka gani, Mutum dan Adam ne a cikinta yanda suma wadanda suka ki karbar haihuwarta suke mutane, Su tuna suna da yaya, kanne da jikoki, Kuma irin haka zai iya faruwa dasu ko Allah ya jarabce su da wata jarabawa ko wani ibtila'i toh ya kake tsammani zasu ji."

Kara karanta wannan

Kaico: Jinkirin 'alert' yasa ikitoci sun ki kula mata mai juna biyu, sun barta ta mutu a Kano

CBN da al'ummar Najeriya

Sama makonni biyu kenan yan Najeriya na fama da karancin takardun Naira tun bayan tilasta yan Najeriya mayar da tsaffin kudadensu banki.

Gwamnonin Najeriya sun bukaci shugaban kasa ya soke wannan tsari saboda al'ummarsu na shan bakar wahala.

Shugaba Buhari ya bukaci su bashi kwanaki 7 zai magance lamarin. Amma bayan kwanaki bakwan, babu wani saukin da abun yayi.

A ranar karewar wa'adin, shugaba Buhari ya kira taron majalisar magabata da masu ruwa da tsaki inda suka bayyana nasu shawarin.

Sun ce gwamnan CBN ya buga isassun sabbin kudi ko ya fito da tsaffi mutane suyi amfani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel