Tsohon Abokin Takarar Buhari Ya Bayyana Abin da Suka Tattauna da Tinubu
- Fasto Tunde Bakare wanda suka taɓa yin takara tare da Muhammadu Buhari ya yi magana kan ziyarar da ya kai wa Bola Tinubu
- Ya bayyana cewa sun tattauna batutuwa da yawa a yayin ziyarar da ya kai wa shugaban ƙasan a gidansa da ke birnin Legas
- Fasto Bakare mai shekaru 70 a duniya ya ce yana da fatan ganin cewa Najeriya ta samu ci gaban da ya dace a lokacin da yake raye
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Fasto Tunde Bakare, wanda ya kafa Cocin Citadel Global Community Church, ya bayyana dalilin da ya sa ya kai ziyara ga Shugaba Bola Tinubu a Legas.
Fasto Tunde Bakare dai ya kai ziyara ga shugaban ƙasan ne a gidansa da ke Legas.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Fasto Bakare ya ce tattaunawarsu ta mayar da hankali ne kan yadda Najeriya za ta inganta a zamaninsa.

Kara karanta wannan
Bola Tinubu ya karɓi bakuncin fitaccen malami, Tunde Bakare, an ji abin da suka tattauna
Fasto Bakare ya kai wannan ziyara ne kwanaki 45 bayan da ya soki gwamnatin Tinubu a jawabinsa na cikin watan Afrilu.
A wancan lokacin, Fasto Bakare ya gargadi shugaban ƙasa da kada ya riƙa ɗaukar kansa kamar ya fi kowa, yana mai cewa gwamnatinsa ta kauce kan hanyar da ta dace.
Me Bakare ya tattauna da Bola Tinubu?
Duk da cewa ya nuna jin daɗinsa da yadda shugaban kasa ya karɓe shi, ya ƙi bayyana cikakken abin da suka tattauna.
"Ziyarata ga Shugaba Tinubu na da nasaba da yadda za a tabbatar da ci gaban ƙasar nan."
"Manufata ta rayuwa ita ce na ga Najeriya ta zama ƙasa mai inganci a lokacin da na ke raye, kuma waɗannan ne abubuwan da muka tattauna da shugaban ƙasa."
“Ba ɓoyayyun abubuwa ba ne, amma na koyi cewa idan ka yi magana da wanda ke da iko, ka bar shi ya yanke hukunci kan yadda zai yi da shawarar da ka ba shi."
"Na yi tattaunawa ta sirri da shugaban ƙasa, kuma na ji daɗi da yadda ya tarbe ni. Ina da tabbacin cewa Allah zai taimaka wa ƙasarmu."
“Abin da muka tattauna ya kasance tsakanina da shi. Da yardar Allah, za a samu nasarar kawo sauyi a kasar nan domin kada ta rushe, a maimakon haka, ta farfaɗo, ta yadda Shugaba Tinubu zai bar tarihi mai kyau wanda ba za a iya gogewa ba.”
- Fasto Tunde Bakare
Fasto Bakare na son Najeriya ta ci gaba
Fasto Bakare ya bayyana burinsa kan Najeriya, yana mai cewa lokaci ya yi da ƙasar za ta ɗauki matakan ci gaba, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Source: Twitter
“Ina so na ga ƙasa mai zaman lafiya. Ina so na ga ƴan Najeriya suna riƙon juna da amana. Ina so na ga haɗin gwiwa mai kyau tsakanin Arewa da Kudu domin jagorantar Najeriya zuwa tafarki mai kyau."
“Ina so na ga ci gaba mai tabbaci a cikin ƙasar mu. Mun yi ta kwan gaba kwan baya kan wasu batutuwa na dogon lokaci, lokaci ya yi da za mu ɗauki mataki na zahiri."
- Fasto Tunde Bakare
Minista ya kwarzanta gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya ƙwararo yabo ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ministan ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta cimma abubuwan da sauran gwamnatocin da suka gabace ta ba su cimmawa ba.
Mohammed Idris ya nuna cewa tuni manufofin gwamnatin suka fara haifar da ɗa mai ido wajen bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

