Sheikh Gumi Ya Yi Magana yayin da aka Hana Shi Shiga Saudiyya Aikin Hajji

Sheikh Gumi Ya Yi Magana yayin da aka Hana Shi Shiga Saudiyya Aikin Hajji

  • Dr Ahmad Gumi ya yi magana kan aikin Hajjin shekarar 2025 saboda zargin hukumomin Saudiyya da kawo masa cikas
  • Malamin ya yi zargin cewa bayyana ra’ayinsa kan siyasar duniya ne suka sa aka nuna rashin gamsuwa da zuwansa Hajji
  • Sheikh Gumi ya gode wa gwamnatin Najeriya da ta tsaya masa, ya ce yanzu zai mayar da hankali kan lafiyarsa da harkokin noma

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya bayyana cewa ba zai samu zuwa aikin Hajji a bana ba.

Sheikh Ahmad Gumi ya ce rashin samun damar zuwansa Hajji na da alaka da matsalolin da ya fuskanta daga hukumomin Saudiyya.

Sheikh Gumi
An hana Sheikh Gumi shiga Saudiyya aikin Hajji. Hoto: Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Twitter

Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da malamain ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Su wanene ke juya akalar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu? Minista ya koro bayani

Ahmad Gumi ya ce an hana shi yin Hajji

A cikin sanarwar da ya wallafa, Dr Gumi ya ce an ba shi takardar izinin Hajji tun farko, amma daga bisani Saudiyya ta nuna rashin jin daɗinta da kasancewarsa a ƙasar.

Sai dai ya ce gwamnatin Najeriya ta nuna jajircewa wajen kare ‘yancinsa, inda ta dauki mataki na tuntuɓar hukumomin Saudiyya kan batun, a matsayin kare dimokuraɗiyya da ‘yancin addini.

Gumi zai koma gona bayan gaza zuwa Hajji

Dr Gumi ya bayyana cewa duk da bai samu zuwa aikin Hajji a zahiri ba, ya samu kammala aikin a zuciyarsa da kuma niyyar da yake da ita.

Ya ce yanzu yana gida a Najeriya, kuma zai ci gaba da kula da lafiyarsa da kuma harkokin noma da ya saba da su.

Sheikh Gumi na cikin Malaman Najeriya da ke sukan Saudiyya a kan lamuran da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, musamman a Gaza.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba za ta magance matsalar ruwa, an fitar da biliyoyi domin noman rani

Mutane sun yi magana bayan hana Gumi zuwa hajj

Bayanin Dr Gumi ya haifar da martani daga Mustapha Jafar, wanda ya ce hana shi aikin Hajji ya tabbatar da cewa Saudiyya na nuna damuwa da malamai masu yin magana kan gazawarta.

Mustapha ya ce wannan lamari ya nuna cewa malamai da ke fadin gaskiya ake tsoratawa, kuma ya ja hankalin sauran malamai da su duba matsayayarsu kan fadin gaskiya.

Ya kara da cewa gwamnatin Najeriya ta fi ta Saudiyya hangen nesa, domin har yanzu Gumi na sukar gwamnati, amma an ba shi matsayi a cikin malamai masu koyar da alhazai.

Sheikh Gumi
Najeriya ta shiga lamarin hana Sheikh Gumi zuwa aikin Hajji. Hoto: Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Kira ga addu’a kan hana Gumi zuwa Hajji

Mustapha Jafar ya bayyana cewa wannan lamari darasi ne babba, ya nuna cewa Saudiyya ta yanzu ta bambanta da ta baya, kuma akwai bukatar addu’a gare su domin samun shiriya.

A karshe, ya jaddada cewa duk da ƙoƙarin hana Gumi shiga Saudiyya, Allah zai karfi aikin Hajjinsa saboda niyyarsa mai kyau.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da shari'arta da gwamnati, an nemi Hamdiyya an rasa a birnin Sokoto

An taba hana gumi zuwa Saudiyya?

Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, daya daga cikin fitattun malaman addinin Musulunci a Najeriya, ya sha fuskantar matsaloli daga hukumomin Saudiyya dangane da shiga kasar domin gudanar da ibada, musamman aikin Hajji.

Wannan ba shi ne karo na farko da aka samu rahoton hana shi izinin shiga ba.

A baya ma, an taba hana shi shiga Saudiyya, musamman bayan bayyana ra’ayoyinsa game da siyasar Gabas ta Tsakiya da matakan da Saudiyya ke dauka a kan kasashe irin su Yemen da Falasɗinu, lamarin da bai yi wa hukumomin Saudiyya dadi ba.

Ba Sheikh Gumi ne malamain farko da Saudiyya ta haramtawa izinin shiga ba, akwai da dama daga kasashe daban-daban..

Haka zalika, a duniya baki ɗaya, malamai irin su Sheikh Yusuf al-Qaradawi daga Qatar da wasu daga Iran sun sha fuskantar irin wannan.

Wannan matsala ta Gumi ta sake jaddada yadda ra’ayi ko fatawa na iya zama dalilin takura ko hana malamai damar gudanar da ibada a kasa mai alhakin masallatai biyu masu alfarma.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun nuna bajinta a duniya wajen bikin 'yancin kasar Kamaru

HAHCON ta gargaji mahajjatan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar alhazan Najeriya ta NAHCON ta gargadi mahajjatan Najeriya yayin da suke isa kasa mai tsarki.

Hukumar ta yi kira ga dukkan mahajjatan da su rika girmama doka da yin abubuwan da suka kamata a kasar.

NAHCON ta fadi haka ne domin tattabar da cewa mahajjatan Najeriya sun yi aikin Hajji lami lafiya ba tare da wata tangarda ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng