Yadda 'Yan Bindiga Suka Karbi N11m, Suka Kashe Limami da Iyalansa cikin Wulakanci
- Limamin Jumma’ar Maru da wasu ƴan gidansa sun mutu a hannun ƴan bindiga bayan kwashe watanni a cikin daji
- An ce ƴan bindigar sun yi amfani da dutse mai zafi wajen azabtar da jikansa mai shekara biyu har malamin ya mutu
- Duk da an biya Naira miliyan 11, ba a sako duka mutanen da aka sace ba, wasu na nan a hannun masu garkuwa da mutanen
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - An bayyana irin azabar da iyalan limamin jumma’a na Maru suka sha a hannun ƴan bindiga kafin kashe su.
An sace limamin, Salihu Suleiman, wanda tsohon alkalin kotun Shari’a ne tare da wasu mutum 23 ciki har da sababbin ma’aurata.

Source: Facebook
Amnesty International ta wallafa a X cewa cikin waɗanda aka sace har da matarsa, ƴaƴansa mata uku, ƴaƴansa maza uku da ɗan jikansa mai shekara biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin iyalansa da aka sace, ƴaƴansa Kabiru da Khuzaifa, da kuma jikan nasa sun mutu a hannun barayin.
Duk da kudin fansa da aka biya, wasu daga cikin waɗanda aka sace har yanzu suna hannun ƴan bindigar, inda ba a da tabbacin ko za su tsira.
Maganar biyan kudin fansan limami
Ƴan bindigar sun nemi Naira miliyan 70 kafin su sako waɗanda suka sace, amma daga baya bayan tattaunawa da addu’o’i, an rage kudin zuwa Naira miliyan 11, wanda daga bisani aka biya.
A lokacin da aka sace Limamin, yana fama da rashin lafiya, kuma iyalansa suna kai masa magani da kaya a daji bayan ƴan bindigar sun nema.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar ko rashin lafiyar tasa ce ta kashe shi ko kuma an kashe shi da gangan ba.
Ɗan shekara 2 ya mutu bayan azabar 'yan bindiga
Wani surukin limamin mai suna Muhammadu ya bayyana yadda suka sha wahala a hannun ƴan bindigar.
Muhammadu ya ce:
“Baba yana fama da rashin lafiya tun kafin a kama shi. Abin da ya gani na azabar da aka yi wa iyalinsa ya tayar masa da hankali.”
Daily Trust ta wallafa cewa Muhammadu ya ce:
“Ƴan bindigar sun aza dutse mai zafi a tafin hannun ɗana mai shekara biyu har sai da ya mutu yana kuka.”
Haka kuma, Kabiru da Khuzaifa, ƴaƴan Limamin, sun sha irin wannan azabar kafin a kashe su a cewar Muhammadu:
“Wani lokaci da wuya in iya tunawa da wasu abubuwa saboda irin tsananin baƙin ciki.”
Amnesty International ta yi Allah-wadai
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta fitar da sanarwa tana Allah-wadai da wannan kisan gilla da azabar da aka yi wa limamin da ƴaƴansa.
Amnesty ta ce:
“An kama su ne cikin watan Maris, lokacin azumin Ramadan, kuma ana azabtar da su kullum ba tare da isasshen abinci ko ruwa ba.”

Source: Facebook
Amnesty ta bukaci gwamnati ta gaggauta kawo ƙarshen waɗannan hare-hare da kashe-kashen da suka zama ruwan dare a jihar Zamfara.
An kama tsohon sojan Birtaniya a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa an kama wani tsohon sojan Birtaniya a Najeriya kan safarar makamai.
An kama mutumin ne a kan zargin safarar makamai da suka hada da bindigogi kirar AK 47 sama da 50 da tarin harsashi.
Rahotanni sun nuna cewa Birtaniya ta bayyana cewa ba ta da alaka da tsohon sojan a yanzu duk da cewa ya taba aiki da ita a shekarun baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


