Bayan Kashe Limamin Masallain Juma'a, An Sake Kashe Wani Makiyayi a Filato

Bayan Kashe Limamin Masallain Juma'a, An Sake Kashe Wani Makiyayi a Filato

  • Labari mara dadi ya sake fitowa daga Karamar Hukumar Bokkos da ke jihar Filato inda aka kashe wani makiyayi mai suna Nuhu Adamu
  • Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu mahara da ba a sani ba sun halaka babban limamin Juma'a na kauyen Ndun a karamar hukumar Bokkos
  • Garba Abdullahi, Shugaban Kungiyar Gang Allah Fulani Development Association (GFADAN) ya tabbatar da kisan Nuhu da ya ce ya faru ne a lokacin yana dawowa daga gonarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Filato - Rahotanni da suke fitowa nuna ce an kashe wani makiyayi mai suna Nuhu Adamu a unguwar Mortal da ke Bokkos a jihar Filato.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan kashe babban limamin Juma'a na Kauyen Ndun da ke yankin Tangur na Karamar Hukumar Bokkos a jihar, Malam Muhammad Sani Idris, da wani dan acaba, Muhammad Gambo.

Kara karanta wannan

Don burge Bankin Duniya: An tona asirin dalilin Tinubu na kara farashin mai da wutar lantarki

Caleb Muftwang
An Sake Kashe Wani Makiyayi a Filato. Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Shugaban kungiyar GAFDAN ya tabbatar da lamarin

Shugaban kungiyar Gang Allah Fulani Development Association of Nigeria (GAFDAN), Garba Abdullahi, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce an gano gonar a ranar Alhamis a unguwar Mortal, kasa da kilomita biyu daga Ndun, inda aka kashe babban limamin da kaninsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ciyaman din ya yi bayani cewa maharan sun tare Nuhu ne a yankin yayin da ya ke dawowa daga gonarsa, ya kara da cewa kungiyar ta sanar da jami'an Operation Safe Haven da yan sanda a Bokkos.

Daily Trust ta rahoto cewa kimamin mutane 23 yan kauyen Bokkos aka kai wa hari a jajiberin Kirsimeti, inda aka hallaka fiye da mutane 150.

Jami'an tsaro da suka hada da sojojin kasa, sojojin sama, sojojin ruwa da yan sanda sun sha alwashin kawo karshen hari da ramuwar gayya tsakanin manoma da makiyaya bayan kashe-kashe a Bokkos da Barkin Ladi.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Mutum uku da aka sace sun mutu a kokarin gudowa daga hannun yan bindiga

Karin Bayani Na Nan Tafe ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel