Limamin masallacin juma'a ya sha da kyar a hannun mafusatan masallata

Limamin masallacin juma'a ya sha da kyar a hannun mafusatan masallata

Jami'an tsaro kasar Sudan sun taimakawa wani fitaccen malamin addinin musulunci ficewa daga masallacin juma'a a lokacin da yake tsakar yin huduba, sakamakon yunkurin far ma sa da masu zanga-zanga suka yi matukar bai jagoranci boren da suke yi ba.

Matasan dai na zanga-zanga ne kan matsalar tsadar Burodi da bukatar shugaban kasar Sudan Omar el-Bashir ya sauka daga mulkin kasar da ya shafe shekaru aru-aru yana yi.

Limamin masallacin juma'a ya sha da kyar a hannun mafusatan masallata
Limamin masallacin juma'a ya sha da kyar a hannun mafusatan masallata
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Barayi sun shiga ofisoshin 'yan majalisar tarayya 3

A wani hoton bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta, an nuna wani mutum yana yi wa Imam Abdul Hai Yusuf da ake zargin da goyon bayan gwamnati ihu tare da bukatar da ya jagoranci masu zanga-zangar.

Hatsaniya ta kaure ne a daidai lokacin da daya daga cikin mahalarta sallar juma'a a babban masallacin da ke al-Halfaya Bahri a arewacin Sudan, ya tashi yana kalubalantar Imam Abdul Hai Yusuf saboda tun fara boren malmin bai ce uffan ba.

'Yan sanda dai sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar da suka yamutsa masallacin juma'ar da rera waken kin jinin gwamnati, da kokarin tilastawa Imam Abdoul Hai Yusuf ya jagoranci boren na ranar Juma'a.

Baya ga birnin Khartoum, lamari irin hakan ya kuma faru a wani masallacin juma'a da ke Sayed Abdel Rahman a birnin Khartoum da birnin Omdurman. Jami'an tsaro sun ce babu wanda ya mutu sai dai jikkata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel