Taraba da Sauran Jihohin da ke karkashin Mulkin Jam'iyyar PDP tun Shekarar 1999

Taraba da Sauran Jihohin da ke karkashin Mulkin Jam'iyyar PDP tun Shekarar 1999

Tun bayan komawar Najeriya zuwa mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, akwai jihohi guda shida da PDP ke mulki ba tare da wata tangarda ko sauya jam’iyya ba.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –. Duk da canje-canje da rikice-rikicen siyasa da kuma karuwar tasirin jam’iyyar hamayya irin su APC, wadannan jihohi ba su taba zaben gwamna daga wata jam’iyya ba face PDP.

Gwamna
Wasu daga cikin gwamnonin PDP Hoto: Agbu Kefas/Umo Eno/Ewo Emo Uno
Source: Facebook

Ga cikakken bayani kan kowace jihar PDP:

1. Taraba

Jihar Taraba da ke Arewa maso Gabas ita ce daya daga cikin jihohin Arewa da PDP ke mulki tun 1999 ba tare da ta samu matsala ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk gwamnonin da jihar ta samu tun daga mulkin dimokuradiyya sun fito ne daga jam’iyyar PDP, kuma yanzu haka Agbu Kefas ne gwamna.

Kara karanta wannan

Obi, Okowa da mutanen da Atiku ya jawo jiki, amma suka fice daga PDP suka bar shi

Leadership ta wallafa cewa daga cikin gwamnonin PDP da suka jagoranci Taraba akwai Jolly Nyame (1999–2007), Danbaba Suntai (2007–2015), Darius Ishaku (2015–2023) da kuma Agbu Kefas (2023–yanzu).

2. Akwa Ibom

Akwa Ibom na daga cikin manyan jihohin da PDP take da tasiri tun a shekarar 1999 ba tare da ta samu tangarda ba, duk da jam'iyyar ta rasa kujerar shugaban kasa bayan mulkin shekaru 16.

Daga cikin fitattun shugabannin PDP da jihar ta fitar har da Sanata Godswill Akpabio da ya koma APC daga baya.

Yanzu haka Umo Eno ne gwamnan jihar, amma kafin shi akwai Victor Attah (1999–2007), Godswill Akpabio (2007–2015), Udom Emmanuel (2015–2023) da Umo Eno (2023–yanzu).

Intel Region ta ruwaito cewa idan gwamna Eno ya koma APC kamar yadda ya yi ikirari, wannan zai kawo karshen mulkin PDP a jihar.

3. Bayelsa

Bayelsa ita ce jiharta tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, kuma PDP ta fuskanci kalubale da dama a can, ciki har da shari’o’i a kan zabukan jihar.

Duk da haka, PDP ba ta taba rasa mulki ba, ko a lokacin da Timipre Sylva ya fice daga PDP, dama a jam’iyyar ya fara mulki, kuma kotu ta tabbatar da ci gaba da mulkin PDP.

Kara karanta wannan

'Saura kiris': Gwamna ya tabbatar da shirin komawa APC bayan jita jitar barin PDP

A yanzu Douye Diri ne ke jagorancin jihar, kuma kafin mulkinsa an samu Diepreye Alamieyeseigha (1999–2005), Goodluck Jonathan (2005–2007).

Sannan akwai Timipre Sylva da ya yi mulki daga 2007–2012 kafin ya sauya sheka, sai Henry Seriake Dickson (2012–2020) da kuma Douye Diri (2020–yanzu).

APC ta ci zaben gwamnan Bayelsa a 2019, amma kafin a kai ga rantsar da David Lyon, kotu ta rusa nasararsa saboda matsalar takardun karatu.

4. Enugu

Enugu na daga cikin jihohin PDP a yankin Kudu maso Gabas da mutanenta ba su taba sauya jam’iyyar gwamnansu ba tun 1999.

Duk zabe, jam’iyyar na lashe kujerun gwamnati da na 'yan majalisa rututu, kuma a yanzu haka Peter Mbah ne gwamnan jihar a yanzu.

Gabanin Mbah, Chimaroke Nnamani ya yi gwamnan jihar daga 1999–2007, Sullivan Chime (2007–2015) da kuma Ifeanyi Ugwuanyi (2015–2023).

Ribas ta taba kubucewa jam'iyyar PDP

Jihar Ribas ta fuskanci rikicin sauya jam’iyya lokacin da Rotimi Amaechi ya fice daga PDP zuwa APC a 2013 bayan shekaru kusan 14 ta na mulki.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta yi babban kamu ana tsaka da batun sauya sheƙar gwamnan Delta

PDP ta sake lashe zaben 2015 da 2019 a karkashin Nyesom Wike, sannan ta sake kafa gwamnati a 2023 da Siminalayi Fubara da Bola Tinubu ya dakatar.

Fubara
Gwamnan PDP da Tinubu ya dakatar Siminalayi Fubara Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Source: Facebook

Duk da rikice-rikicen da ake samu a jihar, PDP bata taba faduwa zaben gwamna ba, inda ta zabi Peter Odili (1999–2007).

Kafin shi akwai Celestine Omehia (May–Oct 2007), Rotimi Amaechi (2007–2015 — ya ci zabe da PDP), Nyesom Wike (2015–2023) da Siminalayi Fubara wanda gwamnatin tarayya ta dakatar.

Yadda PDP ta rasa Delta

Delta ba ta taba zaben gwamna daga wata jam’iyya ba sai PDP tun 1999, duk da cewa a wannan shekara, an samu matsala saboda sauya shekar gwamnanta.

Jihar na daya daga cikin wuraren da PDP ke da cikakken iko, inda manyan ‘yan siyasa kamar James Ibori da Ifeanyi Okowa suka taka rawa a tsarin mulki da jam’iyyar.

Jerin gwamnonin Delta sun hada da James Ibori (1999–2007), Emmanuel Uduaghan (2007–2015), Ifeanyi Okowa (2015–2023) da Sheriff Oborevwori da ya sauya sheka zuwa APC.

Wadannan jihohi shida — Akwa Ibom, Bayelsa, Delta, Enugu, Rivers da Taraba — su ne kadai a Najeriya da PDP ta ci gaba da mulki cikakke tun 1999 har zuwa 2023.

Kara karanta wannan

Siyasa rigar 'yanci: Jerin gwamnonin PDP da suka koma APC suna kan mulki

Baya ga Delta da ta koma hannun APC, ana fargabar Akwa Ibom ta kusa fadawa hannun APC, musamman bayan kalaman gwamnan da tayin da ake yi masa.

EFCC ta tabo batun tsohon gwamnan PDP

A wani labarin, kun ji cewa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya roƙi ƴan Najeriya da su yi haƙuri kan yadda suke gudanar da aikinsu.

Shugaban na EFCC ya bayyana hakan ne musamman a kan yadda ta ke gudanar da aikinta, musamman wajen shari’o’in da suka shafi manyan mutane da masu ƙarfi a siyasa.

Ya ƙara da cewa dole ne ƴan Najeriya su fahimci cewa shari’o’in da suka shafi manyan mutane kamar su Ifeanyi Okowa ba su da sauƙi, domin ana amfani da dabaru don gujewa hukunci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng