Zaben Bayelsa: Takaitaccen tarihin rayuwa da labarin David Lyon Perewonrimi

Zaben Bayelsa: Takaitaccen tarihin rayuwa da labarin David Lyon Perewonrimi

Mista David Lyon ne wanda ya lashe zaben sabon gwamnan jihar Bayelsa. ‘Dan takarar jam’iyyar hamayyar ya doke sauran Abokan gabar siyasa 44 a zaben da ya gabata a karshen makon jiya.

Sabon gwamnan mai jiran-gado ba sananne ba ne a siyasa, amma ya rushe daular da jam’iyyar PDP ta kafa tun 1999. Shekaru 20 kenan ba a samu jam’iyyar adawa ta mulki Bayelsa ba sai yanzu.

Mun tsakuro maku wasu kadan daga cikin abubuwan da ya dace ku sani game da gwamnan goben:

1. Cikakken sunansa shi ne Mista David Lyon Perewonrimi.

2. An haife sa ne a Ranar 20 ga Watan Disamban 1970 a cikin Kauyen Olugbobiri a jihar Bayelsa.

3. Zababben gwamnan ya fito ne daga cikin mutanen Olodiana na Kabilar Ijaw bayan an haife sa a karamar hukumar Kudancin Ijaw.

4. Ya yi karatun Sakandare a Kauyensa a wata makaranta mai suna Saint Gabriel’s State School daga 1984 zuwa 1988

5. Lyon ya kuma yi karatun gaba da sakandare a kwalejin ilmin jihar Ribas da ke Garin Fatakwal inda ya samu shaidar karatu na NCE.

KU KARANTA: David Lyon shi ne wanda ya lashe zaben Gwamnan Bayelsa

6. David Lyon kasurgumin Attajirin ‘Dan kasuwa ne wanda aka sani da kyauta.

7. Shi ne shugaban kamfanin tsaro na Darlon Security and Guard da ke Bayelsa.

8. Lyon bako ne a siyasa kafin jam’iyyar APC ta tsaida shi takarar Gwamna a 2019.

9. Gwamnan mai jiran gado ya na cikin ‘ya ‘yan PDP har ya taba neman takarar ‘dan majalisar Mazabar Kudancin Ijaw a 2011 amma ya sha kashi.

10. A 2015 ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai adawa.

11. Lyon ya yi takara da mutum 5 a APC wajen samun tikitin gwamna. Daga ciki har da tsohon Minista, Heineken Lokpobiri.

12. Zai hau mulki bai cika shekaru 50 a Duniya ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel