Bikin Sallah: Matakin da Aminu Ado Ya Ɗauka bayan Rasuwar Galadiman Kano
- Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya soke duk wasu shirye-shiryen bukukuwan sallah da aka tsara sakamakon rasuwar Galadima
- Sanarwar da fadarsa ta fitar ta bayyana cewa bukukuwan sallah da za a yi a gidan Nasarawa an soke su saboda wannan babban rashin da aka yi
- A cikin sanarwar, Sarkin Kano ya bayyana alhini, yana cewa Galadiman Kano dattijo ne mai jajircewa da ya ba da gudunmawa ga Kano da Najeriya
- Aminu Ado Bayero ya yi addu’a Allah ya gafarta wa mamacin, ya sa ya huta, tare da yi wa iyalansa da al’ummar Kano fatan hakuri da juriya
- Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Kano - Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya soke tsare-tsaren da ya shirya game da bukukuwan sallah bayan rashin da aka yi.

Kara karanta wannan
"An yi rashi," Shugaba Tinubu ya yi magana da Allah ya karɓi rayuwar Galadiman Kano
Basaraken ya dakatar da duk wasu tsare-tsare da ya shirya na bukukuwan sallah a gidan Nasarawa saboda rasuwar Galadiman Kano.

Asali: Facebook
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Masarautar Kano ya wallafa a manhajar Facebook a jiya Laraba 2 ga watan Maris, 2025.
Galadiman Kano: Abba ya soke tsare-tsaren sallah
Hakan ya biyo bayan matakin da gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir ta dauka na soke wasu shirye-shirye sallah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan rasuwar Galadiman Kano, gwamnatin jihar Kano ta soke gaisuwar karamar Sallah a masarautun Rano da Karaye aka shirya yi.
Gwamnatin Kano ta umurci jami’ai su hallara a gidan gwamnati da karfe 9:30 na safe domin tafiya jana’izar marigayin da aka gudanar da misalin karfe 10:00 na safe.
Marigayin ya rasu ne a ranar Talata 1 ga watan Afrilun 2025 ya na da shekaru 92 bayan ya sha fama da jinya mai tsawo.

Kara karanta wannan
Abin da Buhari ya ce bayan rasuwar dattijo, Galadiman Kano, ya fadi giɓin da ya bari
Al'ummar Kano da ma sauran jihohi sun nuna alhini kan babban rashi da aka yi ciki har da ƴan siyasa da manyan yan kasuwa.

Asali: Facebook
Aminu Ado ya yi alhinin rasuwar Galadiman Kano
A cikin sanarwar, Aminu Ado Bayero ya yi alhinin rashin dattijon inda ya yi masa addu'a ta musamman domin samun rahama.
Ya ce tabbas an yi rashin dattijo a Kano wanda ya ba da gudunmawa mai tsoka ga masarautar, Kano da ma kasa baki daya.
Sanarwar ta ce:
"Assalamu Alaikum.
"Sakamakon rasuwar Galadiman Kano, Mai martaba Sarkin Kano, Alh. Aminu Ado Bayero ya soke dukkan wasu tsare tsaren bukukuwan sallah da ake gudanarwa a gidan Nassarawa.
"Da fatan Allah ya gafarta masa yasa ya huta, yasa bakin wahalar kenan, Ameen."
Buhari ya kaɗu da rasuwar Galadiman Kano
Mun ba ku labarin cewa tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi jimamin rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi.
Galadima shi ne matsayi mafi girma da 'ya'yan sarakunan Kano ke rike wa, kuma ya kasance ginshikin al'ada da tarihin masarautar.
Buhari ya ce marigayin ya zama jigo a ci gaba, da ya haɗa tarihi da zamani tare da taka muhimmiyar rawa a fadar masarautar Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng