Kotu Ta Dauki Mataki kan Shari'ar Mutum 4 Masu Alaka da Bello Turji
- Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar beli da wasu mutum hudu da ake zargi da alaka da gawurtaccen dan ta’adda, Bello Turji
- Mai shari’a Emeka Nwite ya yanke hukunci cewa za a hanzarta shari’ar mutanen hudu, tare da amincewa da bukatar gwamnati na kare shaidun
- Duk da cewa mutum takwas aka lissafa a cikin tuhume-tuhume 11 da ake yi masu, uku daga cikinsu, ciki har da Bello Turji ba su shiga hannu ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
FCT Abuja — Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar beli da wasu mutum hudu da ake zargi da alaka da gawurtaccen dan ta’adda, Bello Turji, suka gabatar.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Emeka Nwite ya ce lauyan gwamnatin tarayya (AGF), wanda ke gurfanar da su, ya gabatar da kwararan hujjoji da suka nuna cewa ba su cancanci beli ba.

Asali: Twitter
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Ministan shari'a ya bayyana cewa sakin mutanen da ake shari'a da su zai zama babbar barazana ga tsaron kasa da kuma shaidun da ke taimaka wa gwamnati.
Turji: Kotu ta amince da bukatar gwamnati
Punch News ta ruwaito cewa Nwite ya yarda da hujjojin lauyan kasa, David Kaswe, wanda ya bayyana cewa ko da yake bayar da beli na hannun kotu ne,dole ne a bi a hankali.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da cewa Mai shari’an ya amince da zargi ne kawai ake wa mutanen, amma ya yi watsi da bukatar beli.
Haka kuma, ya amince da bukatar da Kaswe ya gabatar domin kare shaidun da za su bada bayani a kotu don ceton rayuwarsu daga barazana.
Bayanin kotu kan belin 'abokan' Bello Turji
A yayin yanke hukunci, Mai shari’a Nwite ya bayyana cewa yana sane da tanadin kundin tsarin mulki da ke nuna cewa duk wanda ake tuhuma da laifi bai aikata ba har sai an tabbatar da hakan.
Sai dai ya ce duba da dukkan hujjojin da aka gabatar, dole ne a tabbatar da sahihiyar shari’a kan wadanda ake zargi da ta'addanci.
Tun a ranar 23 ga Disamba, 2024, Mai shari’a Nwite ya bayar da umarnin a tsare wadannan mutum hudu a gidan gyaran hali na Kuje.
Bayan da aka gurfanar da su, sun musanta tuhume-tuhume 11 da ake yi musu da suka shafi ta'addanci, kuma kotu ta daga shari’ar zuwa ranar 10 ga Fabrairu don fara shari’a.
Wadanda ake zargi da alaka da Turji
Mutum hudu da ake zargin su na taimakawa Turji sun hada da Musa Kamarawa, Abubakar Hashimu (wanda aka fi sani da Doctor), Samuel Chinedu da Lucky Chukwuma.
Sun musanta aikata laifukan da ake zarginsu da su bayan an karanto musu tuhume-tuhume 11 da ke kansu.
Duk da cewa sunayen mutum takwas ne a cikin karar, uku daga cikinsu, ciki har da Bello Turji, ba su shiga hannun hukumomi ba.

Asali: Facebook
Bayan da aka kira shari’ar a kotu, sai aka gano cewa mutum hudu ne kawai suka halarta, lamarin da ya sa Mai shari’a ya nemu inda Bashir Abdullahi ya ke.
Amma lauyan gwamnati, Kaswe, ya bayyana cewa Abdullahi ma ya tsere, kuma ba a kai ga gano inda ya shiga ba a yanzu.
Yaran Turji sun sace dan Isiyaka Rabi'u
A wani labarin, kun ji yadda wasu gungun bata-garin ‘yan bindiga da ke da alaka da ƙungiyar Bello Turji suka sace wani matashi da ya bayyana kansa a matsayin ɗan Isiyaka Rabi’u.
A cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, an gano mutumin cikin firgici yana roƙon iyalansa su biya kuɗin fansa domin kubutar da shi, yayin da ake zabga masa bulala.
muhammad malumfashi, babban edita a sashen hausa na legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng