Tanimu Kurfi: Yadda Aka Shigo da Na Hannun Daman Yar’adua Cikin Gwamnatin Tinubu

Tanimu Kurfi: Yadda Aka Shigo da Na Hannun Daman Yar’adua Cikin Gwamnatin Tinubu

Abuja - A tsakiyar makon nan aka ji cewa Tanimu Yakubu Kurfi ya zama sabon Darekta Janar na ofishin kasafin kudin tarayya.

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Tanimu Yakubu Kurfi masanin harkar tattalin arziki ne wanda ya yi aiki a gwamnatoci a mulkin Ummaru Musa Yar’adua.

Shafin Marketscreener ya kawo kadan daga cikin tarihin sabon Darekta Janar na ofishin kasafi wanda ya canji Ben Akaebuze.

Tanimu Yakubu Kurfi
Tanimu Yakubu Kurfi ya samu mukami a gwamnatin Bola Tinubu Hoto: @DOlusegun/www.thecable.ng
Asali: UGC

Karatu da gwagwarmayar Tanimu Yakubu Kurfi

Tun yana matashi, Tanimu Yakubu yana cikin wadanda suka kafa kungiyar dalibai ta NANS lokacin ya fara karatu a jami’ar Bayero.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dole ta sa ya tafi jami’ar Wagner College a New York a kasar Amurka, ya yi digiri a ilmin tattalin arziki da digirgir a ilmin kasuwanci.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: NDLEA ta kama miyagun kwayoyin da aka shirya harkallarsu a sallah a Kano

Tanimu Yakubu Kurfi da Ummaru Yar’adua

Daga 1999 zuwa 2002, shi ne kwamishinan kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki a Katsina, ana cewa ya yi aiki da yake mukamin.

Kurfi ya yi kokarin ganin ayyukan more rayuwa sun samu 70% a kasafin kudin jihar daga baya ya zama mashawarcin shugaban kasa.

Rawar ganin Kurfi a gwamnatin tarayya

A lokacin Tanimu Yakubu Kurfi yana ofis a gwamnatin tarayya aka kirkiro asusun SWF wanda ake amfani da shi wajen ayyuka.

Masanin ya zama mataimakin shugaban ma’aikatan fada kuma daya daga cikin ‘yan kwamitin kula da tattalin arziki a 2007-2010.

Kamar yadda aka rahoto a shafin Oando, Kurfi ya ba da gudumuwa wajen kara adadin gangunan mai bayan sulhu a Neja Delta.

Tun 2003 aka nada shi ya zama shugaban bankin asusun gina gida, ya rike kujerar zuwa 2007 a gwamnatin Olusegun Obasanjo.

Alakar Tanimu Kurfi da Buhari

Kara karanta wannan

Bayan rasa mulkin Kano, a ƙarshe, Tinubu ya naɗa Nasiru Gawuna mukami

Kurfi ya yi aiki a kamfanoni da bankuna kamar Icon Limited (Merchant Bankers) da kamfanin Afri-Projects Consortium (APC).

Masanin yana cikin wadanda suka tsarawa Muhammadu Buhari manufofin tattalin arziki lokacin yakin neman zaben 2014 a APC.

Sannan Kurfi ya jagoranci darektocin kamfanin NNDC kuma shi ne babban mai ba Arewacin Najeriya shawara a kan tattalin arziki.

Bayanai sun nuna Kurfi yana da matsayi a kamfanin fanshon APT Pensions Funds Manager Ltd.

Technomy ta ce ya na cikin darektocin kamfanin kafin ba shi mukamin nan, shi ne shugaban gudanarwa na hukumar KTDMB a Katsina.

…samun kusanci da Bola Tinubu

Sabon darektan ya yi aiki da Muhammadu Buhari a PTF kamar yadda yake da tsohuwar alaka da Yemi Cordoso da Wale Edun.

A zaben 2023, yana cikin darektocin kwamitin yakin neman zaben Tinubu-Shettima bayan alakarsa da Wale Tinubu a kamfanin Oando.

Ana cewa Tanimu Kurfi ya taba auren tsohuwar shugabar NPA, Hadiza Bala Usman.

Kara karanta wannan

Bayan canja taken ƙasa, Tinubu zai karɓi ƙudurin sauya tsarin mulkin Najeriya

Karfin tattalin arzikin Legas a Najeriya

A wani rahoto, kun ji cewa kananan hukumomin Legas sun fi kowane samun kudi daga kason da ake yi a asusun FAAC a kowane wata.

Daidaikun kananan hukumomin Bauchi da Kano ne kurum suke samun kudi sosai daga Arewa, yawanci jihohin kudu sun fi samun kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng