"Karya Ce Tsagwaronta": Hadiza Bala Usman Ta Caccaki Tsohon Ministan Buhari

"Karya Ce Tsagwaronta": Hadiza Bala Usman Ta Caccaki Tsohon Ministan Buhari

  • Hadiza Bala Usman, hadimar shugaban ƙasa Bola Tinubu, ta kira tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi a matsayin maƙaryaci
  • Hadiza, wacce a da ta shugabanci NPA, hukumar da ke ƙarƙashin ma’aikatar Amaechi, tun da farko ta zargi ministan ta kitsa yadda aka kore ta a cikin littafinta
  • Tsohon ministan ya ce Hadiza ba ta faɗi duk abin da ya faru a littafinta ba, amma ta yi martani da cewa har yanzu Amaechi ya kasa daina yin ƙarya

FCT, Abuja - Hadimar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Hadiza Bala Usman, ta caccaki Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri a zamanin tsohuwar gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

A baya Amaechi ya zargi Hadiza da yin ƙarya game da halayensa a cikin littafinta na kwanan nan, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hotuna Sun Bayyana Bayan FG Ta Kaddamar da Motoci Masu Amfani da Iskar Gas

Hadiza ta caccaki Rotimi Amaechi
Hadiza Bala Usman ta yi kira ga Amaechi ya daina karya Hoto: Rotimi Amaechi
Asali: Twitter

Yadda Hadiza Usman ta caccaki Rotimi Amaechi a cikin littafinta

Ku tuna cewa Hadiza ta yi aiki a matsayin manajan daraktan hukumar kula da tashar jiragen ruwa ta Najeriya (NPA), hukumar da ke ƙarƙashin kulawar Amaechi a matsayin ministan sufuri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin littafinta, mai taimaka wa Tinubu ta bayyana irin ƙwarewar da ta samu a matsayinta na shugabar hukumar a ƙarƙashin kulawar Amaechi da kuma yadda ya tabbatar da an tsige ta a matsayin shugabar hukumar NPA.

Hadiza ta cigaba da cewa Amaechi ya buƙaci a cire ta, ta kowane hali saboda riƙon da ya yi mata a zuci, inda ta ƙara da cewa ɗaya daga cikin irin waɗannan abubuwa shi ne ta ki yiwa tsohon ministan kyaututtuka da suka haɗa da kyautar ranar haihuwa.

A martanin da ya mayar kan zargin a kwanakin baya, tsohon gwamnan na jihar Rivers, ya ce littafin Hadiza na cike da ƙarya kuma ya rasa yadda zai yi ya mayar da martani.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Fitaccen Lauyan Najeriya Ya Yi Bayani Kan Nasarar da Tinubu Ya Samu a Kotun Ƙoli

Dalilin da ya sa aka cire Hadiza matsayin MD ta NPA - Amaechi

Amaechi ya ƙara da cewa tsohon shugaban ƙasa Buhari ya amince da cire Hadiza bayan da kwamitin bincike ya same ta da laifi.

Amma a martaninta, Hadiza, wacce a yanzu Shugaba Tinubu ya ba muƙami, ta zargi tsohon ministan da yin ƙarya ga masu sauraronsa, rahoton Daily Nigerian ya tabbatar.

Ta cigaba da cewa baya ga "ƙarawa miya gishiri, sauya gaskiya da kuma ƙarairayi" a cikin jawabin Amaechi, babu wani abu da ba ta yi magana a cikin littafinta ba idan da tsohon ministan ya damu da ya karanta.

Amaechi Ya Yi Magana Bayan Nasarar Tinubu

A wani labarin kuma, tsohon ministan sufuri a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Rotimi Amaechi ya yi magana bayan nasarar Shugaba Tinubu a kotun ƙoli.

Amaechi ya bayyana cewa babu wani abu da zai ce saboda ƴan Najeriya ba su damu da mayar martani kan batutuwa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel