Babbar Sallah: NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyin da Aka Shirya Harkallarsu a Sallah a Kano

Babbar Sallah: NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyin da Aka Shirya Harkallarsu a Sallah a Kano

  • Rundunar NDLEA ta kama wasu kayayyakin miyagun kwayoyi a yankuna daban-daban na jihar Kano a Arewacin Najeriya
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake shirin bikin babbar sallah a dunkyar Musulma baki daya
  • Hukumar ta bayyana yadda ta tsara tafiyar da lamurra yayin da ta yiwa ‘yan jihar fatan alheri a bikin sallah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Kano - Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), reshen Jihar Kano ta ce ta kama kwayoyin Tramadol guda 230,600 da kuma wasu mutane 106 da ake zargi da hannu a fataucinsu a jihar Kano.

An kama masu safarar kwaya a Kano
An kama masu shirin siyar da kwaya a bikin sallah a Kano | Hoto: NDLEA
Asali: Twitter

Kakakin rundunar, Abubakar Idris-Ahmad, ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Asabar a Kano cewa:

Kara karanta wannan

Hajji 2024: Hukumomin Saudiyya sun kwamushe mutum 18 bisa karya dokar aikin Hajji

“Tsakanin ranakun 10 zuwa 13 ga watan Yuni, a yayin wani samamen da rundunar ta kai kafin bikin babbar sallah, ta kama kwayoyin Tramadol guda 230,600 a hanyar Zaria zuwa Kano.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama manyan masu harkallar kwaya

Ya bayyana cewa, hukumar ta kama mutane 106 maza, inda aka gano cewa 11 daga cikinsu suna cikin manyan dillalan miyagun kwayoyi a kasar nan, Daily Nigerian ta tattaro.

“An kama wadanda ake zargin ne a wurare daban-daban da ake zargin ana harkallar kwayoyi ciki har da Filin Wasan Sani Abacha, Karkasara, Cibiyar Matasa ta Sani Abacha, Dorayi, Makabartar Dan-Agundi, Filin Wasan Brigade Mini da kuma shahararren wajen da ake kira Filin Idi.”

Kayayyakin da aka kwato sun hada da tabar wiwi, miyagun kayan maye na shaka, kwayoyin exol, ruwan maganin codeine da wasu sauran miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan

Badaƙalar N1.85bn: Kotu ta tasa ƙeyar jami'an gwamnatin tarayya zuwa gidan yari

Za a yi bikin sallah da kwayoyi a Kano

Abubakar ya kara da cewa:

“Wadannan miyagun kwayoyi an gano an tara su ne don rabawa da kuma amfani da su yayin bikin babbar sallah.
“Rundunar NDLEA ta Kano ta kuduri aniyar kawar da matsalar sha da fataucin miyagun kwayoyi a jihar.”

Shugaban rundunar ya kuma yi fatan alheri ga al'ummar jihar Kano a yayin bikin sallah tare zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Wani kamun da aka yi a Kano bara

A wani labarin, NDLEA ta yi nasarar kame wasu bata garin da ake zargin suna harkallar miyagun kwayoyi a jihar Kano.

Rahoton da muke samu daga Channels Tv ya bayyana cewa, akalla mutane 619 ne aka kama da miyagun kwayoyin a yankin Sabon Gari da ke jihar.

Wannan na fitowa ne daga bakin kwamandan hukumar na jihar, Abubakar Idris a lokacin da yake zantawa da gidan talabijin din.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.