An Gina Tasha Mai Otel, Gareji da Ofisoshi da Za Ta Rika Daukar Motoci 5000 a Rana

An Gina Tasha Mai Otel, Gareji da Ofisoshi da Za Ta Rika Daukar Motoci 5000 a Rana

  • Ministan sufurin Najeriya, Sanata Sa'idu Ahmad Alkali ya kaddamar da babbar tashar zamani a jihar Gombe a jiya Talata
  • Tashar za ta zama matattara ga dukkan tashoshin mota a jihar ciki har da manyan motoci domin saukaka harkokin sufuri
  • Bikin kaddamar da tashar na daya daga cikin ayyukan da gwamnan jihar ya yi domin murnar cikarsa shekara biyar a karaga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - An kaddamar da babbar tashar zamani wacce aka sanyawa suna 'Tashar Ibrahim Hassan Dankwambo' a Gombe.

Tashar Gombe
Ministan sufuri ya kaddamar da tashar zamani a Gombe. Hoto: Sai'idu Ahmed Alkali
Asali: Facebook

Ministan sufuri, Sanata Sa'idu Ahmad Alkali ne ya kaddamar da tashar kamar yadda wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Masarautu: 'Karya ne' Gwamnati ta yi martani kan rahoton tashin hankali Kano

Gwamnan jihar, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya tabbatar da cewa tashar na cikin ayyukan da ya kaddamar domin murnar cika shekaru biyar a mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwan da tashar Gombe ta kunsa

An gina tashar a tsari na zamani ta yadda aka samar mata da abubuwan more rayuwa kamar otel, asibiti da wuraren gyaran motoci.

Har ila yau, saboda inganta tsaro an samar da ofishin yan sanda, ofishin masu kashe gobara da kuma shagunan sayayya.

Gombe: Dalilin gina tashar a tsarin zamani

A cikin jawabin da ministan ya gabatar, ya nuna cewa an gina tashar ne domin kawo sauki da inganci a harkokin sufuri a Najeriya.

Saboda haka ya bayyana cewa a kowace rana motoci sama da 5000 ne za su rika hada-hada a cikin tashar daga ko ina a fadin Najeriya.

Tashar Dankwambo: Gwamna ya kara haske

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dakatar da muhimmin aikin da Buhari ya fara a Najeriya

A yayin bikin, gwamnan jihar ya ce an radawa tashar sunan tsohon gwamnan jihar 'Tashar Ibrahim Hassan Dankwambo' saboda shi ya fara daura tubalin aikin.

Gwamna Inuwa ya ce hakan na kara nuni da cewa bambancin jam'iyyar siyasa ba zai yi tasirin kawo cikas ga ayyukan cigaba a jihar ba.

A karshe, gwamna Inuwa ya yi godiya ga dukkan wadanda suka taimaka wajen kammala aikin da ya dauki sama da shekaru shida.

Ganduje ya kaddamar da titi a Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Gombe karkashin jagorancin Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ta kaddamar da titi mai sunan Abdullahi Umar Ganduje.

Shugaban jam'iyyar APC ta kasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya halarci bikin kaddamar da titin da kansa tare da gabatar da wasu ayyukan siyasa a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel