An kai hari ofishin jakadancin Najeriya a kasar Canada
Babban ofishin jakadancin Najeriya da ke Ottawa a kasar Canada ya sanar da rufe ofishin jakadanci da ke kasar.
Kazalika, ofishin jakadanci ya ce ya dakatar da duk wasu aiyuka da suka hada da aiyukan gaggawa a ofishin kamar yadda aka saba yi idan bukatar hakan ta taso.
Ofishin jakadancin ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne sakamakon harin da wasu batagari su ka kai ofishin jakadancin tare da raunata wasu ma'aikatan ofishin yayin neman sabunta fasfo.
Hakan na nkunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin ya fitar ranar Laraba kamar yadda jaridar Punch ta wallafa.
Sanarwar ta bayyana cewa, "babban ofishin jakadancin Najeriya a kasar Canada ya na sanar da 'yan Najeriya mazauna kasar Canada da sauran jama'a cewa ya rufe ofishin jakadancin kasar.
"An dakatar da dukkan wasu aiyuka da suka hada da aiyukan gaggawa da ofishin kan yi idan bukatar hakan ta taso.
"Mun fahimci cewa fasfo din dumbin 'yan Najeriya da ke zaune a kasar Canada ya zo kusa da cinye lokacin amfaninsa, a saboda haka akwai bukatar su sabunta.
"Mun bullo da wani tsari na bayar da fifiko ga masu bukata ta gaggawa ko ta musamman domin saukaka aiki.
"Mutanenmu sun gaza girmama wannan tsari, su kan zo su cushe ofishinmu duk ba a bukaci zuwansu ba, saboda ba su da wata matsala ta musamman irin wacce mu ka ambata.
"Ma su neman sabunta fasfo na cigaba da tururuwar zuwa ofishinmu tare da tayar da hankalin ma'aikatanmu ta hanyar cin mutuncinsu, bugun tagogin ginin ofishinmu, zagi, da sauransu.
"Lamarin ya kara lalacewa a ranar Juma'a, 14 ga watan Agusta, 2020, bayan wasu gungun mutane sun taru a bakin ofishin jakadancin tare da hana ma'aikatanmu sauraron mutanen da aka bukaci su zo saboda yanayin uzurinsu.
"Sun kafe a kan cewa dole sai dai mu saurari duk wanda ya zo ofishin.
"Lamarin har ya kai da sun rike wata ma'aikaciyarmu na tsawon mintuna 20 daga kawai zuwa wurinsu domin yi musu bayani, sun ci zarafinta," a cewar sanarwar.
DUBA WANNAN: An sake kai wa tawagar wani gwamnan APC harin bindiga, an kama mutane 15
Kazalika, sanarwar ta ce babu wani ofishi jakadanci da zai yarda da irin wannan halayya ta cin mutuncin ma'aikacinta kamar yadda da mutanen suka aikata.
"Mun rufe ofishinmu na jakadanci domin ganin yadda zamu samar da tsaro a harabar ofishin domin kaucewa halayyar batagari da mabarnata," kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sanarwar ta kara da cewa babu wani dan Najeriya da ke zaune a kasar Canada bisa dalilin karatu ko aiki da zai fuskanci wata matsala ko damuwa saboda karewar amfanin fasfo dinsa.
Ofishin jakadancin ya ce kasar Canada ta sanar da yin sassauci har zuwa karshen shekarar 2020 a kan duk wanda amfanin fasfo dinsa ya kare tun a watan Maris.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng