Muhammadu Sanusi II: Abubuwa 7 da Suka Faru a Rayuwar Sarki Bayan Tube Shi a 2020

Muhammadu Sanusi II: Abubuwa 7 da Suka Faru a Rayuwar Sarki Bayan Tube Shi a 2020

A shekarar 2020 ne gwamnatin Abdullahi Ganduje ta tube Muhammadu Sanusi II daga kurajerar sarautar Kano.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Tube Sarkin ya jawo kace-nace a jihar da ma fadin Najeriya gaba daya saboda ana ganin siyasa ce kawai.

Abubuwan da suka faru bayan tube Sarki Muhammadu Sanusi II daga sarautar a 2020
Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi wasu muhimman abubuwa bayan tube shi a sarautar Kano a 2020. Hoto: : @PDP_Dynasty.
Asali: Twitter

A jiya Alhamis 24 ga watan Mayu, Gwamna Abba Kabir ya dawo da Sanusi II kan kujerarsa, cewar rahoton Daily Trust.

Hakan ya biyo bayan rusa masarautu jihar guda biyar da Ganduje ya kirkiro a 2019 lokacin da ya ke mulkin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hausa Legit ta jero muku abubuwan da suka faru da Muhammadu Sanusi II bayan tube shi da aka yi.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda Muhammadu Sanusi II ya ke maraba da Kanawa a fada duk da halin da ake ciki

1. Korar Sanusi II zuwa kauyen Loko

Bayan tube shi daga sarautar jihar Kano, an kori Sanusi II zuwa kauyen Loko da ke jihar Nasarawa.

Wasu na ganin wannan hukuncin ya yi tsauri da suke dangantawa da siyasa inda daga bisani kotu ta yi hukunci ya samu ƴanci.

2. Koyarwa a Jami'ar Oxford

Bayan samun ƴanci daga kauyen Loko, Sanusi II ya samu koyarwa a Jami'ar Oxford.

An nada Sanusi II a matsayin lakcaran wucin-gadi a African Studies Centre na St. Antony’s College.

3. Kace-nace kan kalmar 'Tsohon Sarki'

Wani abin da ya ja hankalin jama'a shi ne yadda Muhammadu Sanusi II ya ce bai kamata a kira shi da tsohon Sarki ba.

Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce a tarihin masarautar Kano, Sarki zai kasance Sarki ne har abada ko da kuwa ya bar kan kujerar sarauta.

4. Jita-jitar neman shugaban kasa

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II: Jerin manyan sarakunan Arewa da aka tsige a Najeriya tare da dalilai

Sarki Muhammadu Sanusi II a wancan lokaci ya musanta cewa yana harin kujerar shugabancin Najeriya a zaben 2023.

Muhammadu Sanusi II ya ce ba ya bukatar shugabancin kasar inda ya ce mukaman da ya rike sun fi amfani a wajensa kan kujerar shugaban kasa.

5. Ziyara zuwa Jamhuriyar Nijar

Bayan kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum, sojoji sun ki ba da damar tattaunawa amma sun saurari Sanusi II bayan ya je kasar.

Bayan ganawar, Sarkin ya ce matsalar Nijar ba ta gwamnati kadai ba ce ya kamata a hada kai domin a nemo mafita.

6. Mukamin Khalifan Tijjaniya

A shekarar 2021, darikar Tijjaniya ta zabi Muhammadu Sanusi II a matsayin Khalifan marigayi Ibrahim Inyass a kasar Senegal.

Kafin nadin Sanusi II, kujerar ta kasance ba kowa tun 2018 bayan rasuwar Isyaka Rabiu da ya rike muƙamin.

7. Ta'aziyyar Herbert Wigwe

Muhammadu Sanusi II ya nuna alhini sosai bayan mutuwar babban abokinsa kuma tsohon shugaban bankin Access.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya aika sako ga Ganduje bayan ya dawo kan sarautar Kano

Sarkin ya zubar da hawaye wanda ya jawo cece-kuce a fadin kasar baki daya inda aka kalubalance shi kan mutanen da ake kashewa a Arewa.

Muhammadu Sanusi II ya magantu a Kano

Kun ji cewa sabon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi godiya ga Gwamna Abba Kabir bayan dawo da shi kan kujerar sarautar.

Wannan na zuwa ne bayan tube tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna guda hudu a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.