An nada tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido, matsayin khalifan Tijjaniyya a Najeriya

An nada tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido, matsayin khalifan Tijjaniyya a Najeriya

- An gudanar da Maulidin kasa na wannan shekara a cibiyar daular Usmaniyya

- Dubban mabiya darikar Tijjaniya sun samu halartar taron bana

- Muhammadu Sanusi II ya gaji kujeran kakansa Muhammadu Sanusi I

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ya zama jagoran ɗariƙar Tijjaniya a Najeriya.

An yi wannan nadi ne a babban taron Maulidin da ke gudana a jihar Sakkwato.

Khalifan Ibrahim Inyass ne ya jagoranci bikin nada Sanusi.

Sanusi Lamido Sanusi ya gaji kakansa, Muhammadu Sanusi, wanda shine Khalifan Tijjaniyya na farko a Najeriya.

Tun rasuwar tsohon Khalifan Tijjaniya, Sheikh Khalifa Isyaku Rabiu a 2018, ba'a nada wanda zai maye gurbinsa ba sai yanzu.

Taron ya samu halartar manyan shugabannin ɗarikar Tijjaniya a Najeriya da kasashen ketare.

KU DUBA: Daga cikin yan majalisan dokokin tarayya 469, 19 kadai ne mata, ga jerinsu

Kalli bidiyon nadin:

KU KARANTA: Mun nemi kudin makaman da muka baiwa su Buratai mun rasa, NSA Monguno yayi fallasa

A wani labarin daban, wata kotun majistare a jihar Kano ranar Juma'a ta umurci kwamishanan yan sandan jihar ya gudanar da bincike kan zargin barazana da suka da aka daurawa Sheikh Abduljabbar Kabara.

Alkalin kotun, Mustapha Sa’ad-Datti, ya bada wannan umurni ne bayan sauraron karan da Abdulrahman Nasir, lauyan Sheikh Abdallah Pakistan, rahoton NAN.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel