Kauyen Loko: Muhimman abubuwa 7 da ya kamata a sani game da masaukin Sanusi na farko
- Ba sabon labari bane idan aka fadi yadda gwamnatin jihar Kano ta tube rawanin Malam Muhammadu Sanusi II
- Tubabben Sarkin an kara da mayar da shi kauyen Loko da ke jihar Nasarawa inda zai samu mafaka har zuwa karshen rayuwarsa
- Duk da kuwa an sauyawa Sarkin mafaka daga kauyen Loko zuwa Awe ga wasu abubuwa da ba dole mai karatu ya sani ba game da kauyen Loko
Ba sabon labari bane idan aka fadi yadda gwamnatin jihar Kano ta tube rawanin Malam Muhammadu Sanusi II a ranar Litinin, 9 ga watan Maris na 2020.
Tubabben Sarkin an kara da mayar da shi kauyen Loko da ke jihar Nasarawa inda zai samu mafaka har zuwa karshen rayuwarsa.
Duk da kuwa an sauyawa Sarkin mafaka daga kauyen Loko zuwa Awe duk a cikin jihar Nasarawa din, ga wasu abubuwa da ba dole mai karatu ya sani ba game da kauyen Loko da ke jihar Nasarawa.
DUBA WANNAN: Buri na na karshe a rayuwa shine in mutu a kan kujerar sarautar Kano - Sanusi II
1. Kauyen Loko na nan ne a karamar hukumar Nasarawa da ke jihar Nasarawa a Najeriya.
2. Kauyen na nan a wajen gabar kogin Binuwai ne.
3. Kauyen dai ya zamo tamkar karamar tashar jiragen ruwa ne wanda ake diban kaya don haurawa dasu yankunan gabas da yammacin Najeriya.
4. Kabilun da ke kauyen Loko sun hada da Nufawa, Hausawa, Bassa, Igbira, Agatu, Afo da Kanuri.
5. Kauyen yafi karni daya wato shekaru 100 da kafuwa.
6. A halin yanzu Loko na da sarki mai daraja ta daya mai suna Abubakar Sabo Umar.
7. A irin wannan kauyen, noma, kiwo da kamun kifi shine aikin jama'a mazauna garin.
Amma kuma, rahoto daga majiya mai karfi ya tabbatar mana da cewa an shirya tsaf domin dauke tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, daga kauyen Loko zuwa karamar hukumar Awe, ta jihar Nasarawa.
Shugaban maaikatan tsohon sarkin, Munir Sanusi, ya bayyawa DN cewa sun dira gidan gwamnatin jihar yanzu domin garzayawa Awe. Hakazalika, kwamishanan yan sandan jihar, Bola Longe, da shugaban hukumar DSS na jihar, suna gidan gwamnatin domin tarban Sanusi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng