Sarki Sanusi II: Jerin Manyan Sarakunan Arewa da Aka Tsige a Najeriya Tare da Dalilai

Sarki Sanusi II: Jerin Manyan Sarakunan Arewa da Aka Tsige a Najeriya Tare da Dalilai

Sarki Muhammadu Sanusi II ba shi kaɗai ba ne babban basarake mai ƙima da aka taɓa tuɓewa rawanin sarauta a Arewacin Najeriya.

Duk da dai shi Sanusi II ya taki sa'a an sake mayar da shi kan karagar mulki, mafi akasarin sauran sarakunan da aka tsige ba su taki wannan sa'a ba.

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi.
Muhammadu Sanusi II ba shi ne kaɗai sarki a Arewa. da aka taɓa tsigewa ba Hoto: Opeyemtech
Asali: Twitter

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, mun tattaro maku jerin nanyan sarakunan Arewa da aka tsige a Najeriya, ga su kamar haka:

1. Muhammadu Sanusi I

A ranar 28 ga watan Maris, 1963 aka tilasta wa Muhammadu Sanusi na farko (watau kakan Sarki Sanusi II na yanzu) yin murabus daga kujerar sarkin Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanusi II, kakan sarkin Kano na yanzu ya samu saɓani da manyan mambobin NPC a jihar Kaduna, waɗanda suka nuna damuwa da ƙarfin ikon sarkin.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya bayyana rawar da Tinubu ya taka wajen dawo da shi kan sarautar Kano

An kafa wani kwamiti karkashin jagorancin D. J. M. Muffet domin ya binciki yadda aka yi da kudaden gwamnatin Kano a zamanin Sanusi.

Kwamitin ya ba da shawarar cewa sarkin ya yi murabus bayan ya saurari bayanan shedu daga Kano.

A ƙarshe dai Gwamnatin Arewa karkashin jagorancin Kashim Ibrahim ta bukaci Sanusi I da ya yi murabus daga mukaminsa, kuma ya yi ba tare da jayayya ba.

Ya yi sarauta daga ranar 23 ga Disamba, 1953, lokacin da ya zama sarkin Kano na 11 bayan rasuwar Abdullahi Bayero.

2. Mustapha Jokolo

Gwamnan jihar Kebbi a wancan lokacin, Adamu Aliero, ya tsige Mustapha Jokolo, Sarkin Gwandu na 19 a watan Yunin 2005.

An zargi Jokolo da yin kalamai na tunzura wanda ka iya zama illa ga tsaron kasa kuma an tuhumi Sarkin da yin sakaci da aikin sa, sannan ya koma Kaduna da zama tare da iyalansa.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda Muhammadu Sanusi II ya ke maraba da Kanawa a fada duk da halin da ake ciki

3. Ibramin Dasuki

An sauke Ibarahim Dasuki daga matsayin Sarkin Musulmi a Sakkwato ranar 20 ga watan Afrilu, 1996, shekaru takwas bayan hawansa karagar mulki.

Gwamnan Sakkwato a zamanin mulkin soji na wancan lokacin, Yakubu Muazu ne ya kira Dasuki ofis ya faɗa masa cewa an tuɓe shi daga sarauta.

An ce shugaban ƙasa na mulkin soji, Sani Abacha ne ya bayar da umarnin tsige Dasuki. Daga nan aka killace shi a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

A cewar Muazu, abin da Dasuƙi ya aikata ya haifar da tashin hankali a tsakanin jama’a da kuma cikin gidan sarauta.

Ya kuma zargi Sarkin Musulmi na wancan lokacin da yin watsi da umarnin gwamnati.

4. Umaru Tukur

An tube Sarkin Muri, Umaru Tukur daga mukaminsa na sarauta kuma shugaban majalisar masarautar Muri a ranar 12 ga Agusta, 1986.

Gwamnan jihar Gongola a wancan lokacin, Yohana Madaki ne ya tsige sarkin bisa zargin rashin ladabi.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ɗauki zafi, ya ba da umarnin a kama tsohon Sarkin Kano

An tube Tukur shekaru 20 bayan ya zama Sarkin Muri na 11 a 1966. Daga baya gwamnan ya tura tsohon sarkin zuwa Mubi a jihar Adamawa a 1986.

5. Muhammadu Sanusi II

Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya sauke Sanusi II daga sarautar Sarkin Kano a watan Maris, 2020 bisa nuna tsaurin ido da rashin biyayya ga mahukunta.

Sarkin Kano na 14 ya ƙi gurfana a gaban kwamitin da ke bincikensa kan zargin cin hanci da rashawa, bayan da ya samu sabani da gwamnan.

Sai dai kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar da Sanusi II a matsayin Sarkin Kano a ranar 24 ga Mayu, 2024.

Abba ya umarci kama tsohon sarki

A wani rahoton kuma Abba Kabir Yusuf ya bai wa kwamishinan ƴan sanda umarnin kama tsohon sarkin Kano, Aminu Ado Bayero cikin gaggawa.

Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne bisa zargin tsohon sarkin da yunkurin tayar da tarzoma da ruguza zaman lafiya a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262