Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Ya Fashe da Kuka a Wajen Makokin Herbert Wigwe, Bidiyo

Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Ya Fashe da Kuka a Wajen Makokin Herbert Wigwe, Bidiyo

  • Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi, ya fashe da kuka yayin da yake mika ta'aziyyarsa ga iyalan Herbert Wigwe
  • Sanusi ya yi tsokaci a ranar Laraba, 6 ga watan Maris, yayin da yake jawabi ga taron 'yan makoki a bikin birne Wigwe
  • Legit Hausa ta tuna cewa Wigwe yana cikin mutane shida da suka mutu a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a jihar California ta Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Lagos - Muhammadu Sanusi II, tsohon sarkin Kano, ya sharbi kuka yayin da yake jawabi mai tsuma zuciya kan Herbert Wigwe, marigayi shugaban bankin Access a daren ranar Laraba, 6 ga watan Maris.

Wigwe na daya daga cikin mutane shida da suka mutu a ranar 9 ga watan Fabrairun 2023, bayan jirgin sama mai saukar ungulu da suke ciki ya yi hatsari a kusa da Nipton, jihar California, kasar Amurka.

Kara karanta wannan

Dangote ya barke da kuka a wajen makokin Wigwe, ya fadi abu 1 da zai yi domin tuna marigayin

Sanusi ya sharbi kuka kan marigayi Wigwe
Sanusi ya yi jawabi mai tsuma rai kan Herbert Wigwe Hoto: @TundeAremo, @HerbertOWigwe
Asali: Twitter

Yadda Herbert ya shirya mani babban taro - Sanusi

Da yake jawabi ga dandazon jama'a da ke zaman makoki a Lagas, a lokacin bikin birne marigayin, Sanusi ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Da yawa daga cikinku za su tuna a 2021, watan Agusta, a wannan dakin taro, an gudanar da babban taro, na bikin cikana shekaru 60 a duniya da kuma kaddamar da littafina, Herbert ne ya shirya tare da daukar nauyin taron.

Kalli bidiyon wanda Channels TV ta daura a kasa:

Ya ci gaba da cewa:

"Duk wanda ya san Herbert ba tare da ya san wani yabo da aka yiwa Herbert ba, ba gaskiya bane.
"A ranar da ya mutu, na yi wani kasaitaccen biki a Abuja, bani da masaniya kan abin da ke faruwa.
"Na zo filin jirgin sama, ina jiran jirgi, sai na samu kira daga Bola Adesola wanda ta ce, 'Lamido baka ji ba, ba ka ji abin da ya faru da Herbert ba. Sai nace, me? Sai ta ce wannan shine abin da take ji."

Kara karanta wannan

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta nemi a kame dan fafutukar raba Najeriya gida biyu

Na damka dukiyata a hannun Herbert - Sanusi

Sanusi ya ce a cikin shekarar 2022, ya tattara duk kudin da ya mallaka sannan ya mika shi a hannun Wigwe don kula da ilimin yaransa (Sanusi).

Kalamansa:

"Na fada ma Herbert, 'Zan daura ka a kan wannan dukiya don karatun yarana saboda na san cewa koda na mutu, ban bar komai ba, za ka ilimantar da yarana. Ina tunanin zan mutu na bar Herbert."

Dangote ya sha kuka kan mutuwar Herbert

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa an hasko Aliko Dangote yayin da ya barke da kuka a lokacin da yake ta'aziyyar marigayi Herbert Wigwe, tsohon shugaban kamfanin Access Holdings.

Legit Hausa ta ruwaito cewa Wigwe ya mutu ne tare da matarsa ​​da dansa, Chizoba da Chizi, a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a jihar California ta Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel