Dalilin da yasa muke bukatar Sanusi a jami'ar Oxford - Darakta

Dalilin da yasa muke bukatar Sanusi a jami'ar Oxford - Darakta

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya tabbatar wa da jaridar Daily Trust cewa zai fara wani shiri a kasaitacciyar jami'ar Oxford da ke Ingila a watan Oktoban wannan shekarar.

Zai fara karatun ne a cibiyar nazarin Afrika da kwalejin St. Antony duk a jami'ar Oxford.

Kwamitin cibiyar, wanda cikin makon nan ya amince da bukatar Sanusi a cibiyar, ya ce zai yi karatun ne daga 2020 zuwa 2021.

Kamar yadda cibiyar ta ce, Sanusi, wanda aka tube wa rawani a farkon shekarar nan, ya yi niyyar amfani da wannan lokacin don rubuta littafi a kan yadda za a yi martani ga matsalar kudi a duniya.

Cibiyar ta sanar da cewa zai yi amfani da gogewarsa a matsayin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, kuma a matsayin ma'aikacin bankin da gogaggen wanda ya saba mu'amala da jama'a.

A yayin zantawa da Daily Trust a daren jiya, daraktan cibiyar, Farfesa Wale Adabamwi, wanda dan Najeriya ne, ya ce:

"Ina matukar farin ciki da zai zo cikinmu a watan Oktoban. Zai zama babban ci gaba ga abinda muke yi. Zai yi aiki a kan bincikensa kuma zai dinga amfani da gogewarsa don dalibai da manazarta."

Sanusi, masanin tsumi da tattali kuma ma'aikacin bankin, ya yi aiki a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya daga 2009 zuwa 2014.

Dalilin da yasa muke bukatar Sanusi a jami'ar Oxford - Darakta
Dalilin da yasa muke bukatar Sanusi a jami'ar Oxford - Darakta. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Ziyartar Buhari: Gwamnan PDP ya dakatar da masu sarauta 12 a jiharsa

Tsohon darakta janar na hukumar tsaro da musaya, Arunma Oteh, shine babban manazarci a cibiyar a halin yanzu.

Cibiyar ta horar da dalibai wadanda a halin yanzu suke rike da mukamai daban-daban na fannin tattalin arzikin da siyasa a Afrika da sauran sassa na duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel