Yadda Aka Kashe Janar Alkali a Garin Jos – Mai Bayar Da Shaida

Yadda Aka Kashe Janar Alkali a Garin Jos – Mai Bayar Da Shaida

  • Babbar kotun Jos ta fara sauraron shari'a kan kisan gillar da aka yi wa Janar Idris Alkali a Jos, jihar Filato
  • Babban shaida a shari'ar, Manjo Janar Umaru Ibrahim Muhammed (mai ritaya) ya ce kisan wulakanci aka yi wa Janar Alkali sannan aka binne shi a rami bayan a daddatsa gawarsa
  • Jamar Muhammed ya yi bayanin yadda suka shafe makonni suna aikin bincike kafin suka kai ga gano gawar marigayin

Manjo Janar Umaru Ibrahim Muhammed (mai ritaya) ya bayyana yadda aka kashe marigayi Janar Idris Alkali a kauyen Dura-Du, karamar hukumar Jos ta kudu, a jihar Filato.

Janar Muhammed shine wanda rundunar sojojin Najeriya ta daurawa alhakin gudanar da bincike da aikin ceto bayan sanar da batan Janar Alkali a 2018, Daily Trust ta rahoto

Kara karanta wannan

An Gano Bakin Zaren: An Kama Mutum 6 Kan Zargin Kashe Yar Dan Majalisar Borno

Shaida ya koro jawabi kan yadda aka kashe Janar Alkali
Yadda Aka Kashe Janar Alkali a Garin Jos – Mai Bayar Da Shaida Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Babban sojan wanda ya yi bayanin abun da ya gano yayin da ya bayyana a gaban babbar kotun Jos, a ranar Laraba, 25 ga watan Oktoba, a matsayin babban mai bayar da shaida, ya ce an yi wa Janar Alkali kisan gilla ne sannan aka daddatsa gawar shi, kafin aka binne shi a karamin rami.

Yadda aka yi wa Janar Alkali kisan gilla - Shaida

Babban mai bayar da shaidan ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Marigayi Janar Alkali ya bar Abuja da nufin zuwa Bauchi a 2018, yayin da yake kan tafiya, ya yi kiran wayar karshe a wuraren kauyen Dura Du da ke kudancin Jos. Kuma daga wannan lokacin, sai wayarsa ta dauke. Bai isa Bauchi ba kuma ba a sake samunsa a waya ba. Kwanaki uku bayan nan, danginsa suka ayyana batansa, a ranar 3 ga watan Satumban 2018 kenan.

Kara karanta wannan

Janar Alkali: Yadda Shari'ar Kisan Gillar Sojan Ke Wakana a Halin Yanzu, An Gabatar da Wadanda Ake Zargi

"Nine kwamandan runduna ta uku ta sojin Najeriya a wancan lokacin, kuma an daura mun alhakin gudanar da bincike da aikin ceton shi. Aikina uku ne; na gano Janar Alkali a mace ko a raye; na gano motarsa bakar Toyota Corolla mai lamba MUN 679 AA; sannan na gano duk wanda ke da hannu a batansa.
"An hada ni da Manjo Janar daya da dakarun sojoji 30 domin gudanar da wannan aiki. Mun dudduba dukkanin asibitoci, ofishin yan sanda ba tare da sakamako ba. Mun je kamfanin MTN don bincike sannan muka gano cewa wayarsa ta mutu ne a kauyen Dura Du. Ta haka ne muka mayar da akalar bincikenmu a wannan kauyen.
"A kauyen, mun duba kududdugan hakar ma'adinai kusan guda 32, amma bayanan da muka samu yasa muka mayar da hankali kan wani guda daya. Amma sai matasan kauyen suka tattara mata kimanin su 500 domin yin zanga-zanga kan binciken da muke yi. Sai dai duk da turjiyar da yan kauyen suka nuna, mun ci gaba da gudanar da aikinmu.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotu Ta Yankewa Shahararren Likita Da Ya Lalata Yar’uwar Matarsa Daurin Rai Da Rai

"Sai da muka je jihar Taraba muka samo motocin hukumar kashe gobara da wasu masu ruwa a Bauchi da aiki na tsawon makonni biyu, mun yi nasarar kwarfe ruwa daga kududdufin sannan a ranar 29 ga watan Satumba muka gano motar Janar Alkali daga kududdufin. A cikin motar, mun ga inifan dinsa, riga, wando, hula da sunansa a kansu.
"Mun ci gaba da binciken kududdufin, sannan a ranar 1 ga watan Oktoba, muka ga wata motar bas a kududdufin wanda aka ayyana batan direbanta shekaru bakwai da suka gabata. Mun kuma ga wata motar Rova ja, mai motar na zaune a Bisichi, an ayyana batansa a wannan kauyen. Cikin kududdufin akwai motar daukar yashi, kekunan adaidaita, babura da sauransu.
"Kasancewar mun ga motarsa, abu na gaba shine gano gawarsa. Mun karfafa bincike, sannan muka samo daya daga cikin wadanda ake zargin wanda ya jagorance mu zuwa inda makasan suka binne gawar Janar Alkali. Wadanda ake zargin sun bayyana cewa bayan sun kashe Janar Alkali, sun zagaya kauyen da gawarsa kafin suka kai shi wani wuri da ake kira da “No man’s land” sannan aka binne shi a wani rami.

Kara karanta wannan

Yakin Hamas: Ministan Abuja Wike Ya Bayyana Dalilinsa Na Ganawa Da Jakadan Isra’ila a Najeriya

“Daga bisani mun dauko wani kwararren kare daga Abuja, mun gano cewa an riga an dauke gawar daga wajen zuwa wani kauye mai suna Buchwet mai nisan kimanin kilomita 10 daga Dura-Du, mun gano gawar a ranar 30 ga watan Oktoban 2018.
“Binciken kwararru ya gano cewa makasan sun daddatsa gawar Janar Alkali ne, a haka muka ci gaba da bincike da hadin gwiwar iyalansa, har muka tabbatar da cewar gawar tasa ce.
“Binciken ya gano cewa an raba kansa gida biyu, sannan aka daddatsa sauran sassan jikin shi, hakan ne ya tabbatar mana cewa kisan gilla aka yi masa."

An kama mutum 21 kan kisan Janar Alkali

Shaida na biyu, Manjo Arashinga Bulus, jami'in dan sanda mai ci a Abuja, shima ya bayyana rawar ganin da ya taka wajen bincike da tawagar ceton sannan ya tabbatar da cewar an kama mutum 21 da hannu a kisan Janar Alkali.

Kara karanta wannan

Sojojin Sun Share Hawayen 'Yan Arewa, Sun Sheke Kasurgumin Shugaban 'Yan Ta'adda

Bayan sauraron shaidu biyu, kotun ta daga sauraron shari'ar zuwa ranar 6 ga watan Nuwamba, don jin karin bayanai daga wasu shaidun.

An fara sauraron shari'ar kisan Janar Alkali

Da farko Legit Hausa ta rahoto cewa kotu ta fara sauraran shaidu kan shari'ar kisan gilla da aka yi wa Janar Idris Alkali a jihar Plateau.

Babbar kotun da ke zamanta a jihar na ci gaba da sauraran karar ce da safiyar yau Laraba 25 watan Oktoba inda ake zargin mutane 21 da kisan gillar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng