Miyetti Allah ta rufe duka kasuwannin sayar da shanu a Najeriya
Kungiyar makiyaya Fulani ta Najeriya, Miyetti Allah Kautal Horre ta umurci mambobinta su dakatar da kai shanu kasuwanni a dukkan fadin kasar nan.
Kungiyar ta bayar da umurnin ne a daren ranar Litinin yayin wani taron gaggawa da aka gudanar a headkwatan kungiyar da ke babban birnin tarayya, Abuja.
Shugaban kungiyar, Alhaji Bello Abdullahi Bodejo ya shaidawa Daily Trust cewa sun dauki matakin ne sakamakon shawarar da gwamnati ta bawa al'umma na takaita cudanya saboda kare yaduwar annobar Coronavirus.
DUBA WANNAN: Coronavirus: Zahra Buhari ta ce duniya ce ke tsarkake kanta
Bodejo ya ce, "Wannan dokar tana iya kasancewa na tsawon makonni biyu ko uku kafin ayi bita a kan lamarin. Kowa dai ya sani cewa mutane za su iya cin nama ne idan suna cikin koshin lafiya saboda haka ba zai yiwu mu kyalle mutanen mu ba tare da basu shawarwari ba a irin wannan lokacin."
A wani rahoton, kunji cewa gwamnan jihar Plateau Simon Lalong ya bayar da umurnin ma'aikatan gwamnati masu mataki na daya zuwa 12 a jihar su fara yin aiki daga gidajensu sannan kuma a rufe kasuwanni.
Dokar za ta fara aiki daga ranar Laraba 25 ga watan Maris kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
An dauki matakin ne yayin taron gaggawa da majalisar zartarwa na jihar ta yi domin kare yaduwar annobar kwayar cutar Covid-19 da ke kisa ba kakautawa.
Dokar kuma ta ce dukkan masu wuraren shakatawa kamar kulob da mashaya su ma su rufe daga ranar 25 ga wtaan Maris na 2020. Masu sayar da abinci kuma su rika kai wa kwastomominsu abincin gida domin hana cinkoso.
Gwamnan ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu yana saba dokokin sai fuskanci fushin hukuma duba da cewa an bawa hukumomin tsaro umurnin su dauki mataki a kansa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng