Yadda Aka Kusa Hada Ni Fada da Sulhunmu da Gero Argungu Inji Sheikh Dutsen Tanshi

Yadda Aka Kusa Hada Ni Fada da Sulhunmu da Gero Argungu Inji Sheikh Dutsen Tanshi

  • Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya ce shekarun baya wasu su ka hada shi fada da Abubakar Giro Argungu
  • Malamin yake cewa kungiyar Izala ta haddasa rashin jituwa tsakaninsa da wasu malaman musulunci
  • Kafin Sheikh Argungu ya komawa mahallacinsa, sun fahimci juna har malamin ya yi niyyar zuwa Bauchi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Bauchi - Babban malamin nan Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya yi jimamin rashin shehin malamin musulunci, Abubakar Giro Argungu.

A wani karatu da ya yi kwanan nan, Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya tuno da alakarsa da Sheikh Abubakar Giro Argungu da ya rasu.

Malamin addinin mai zama a garin Bauchi ya zargi kungiyar Izala ta reshen jiharsa da jawo rashin fahimta tsakaninsa da shehin da wasu.

Sheikh Dutsen Tanshi
Sheikh Abubakar Giro Argungu Hoto: Ukhashatu Abubakar Gusau
Asali: Facebook

Alaka da Albany da Sa’id Jos

A cewarsa haka kungiyar JIBWIS ta kusa raba shi da Marigayi Muhammad Auwal Adam Adamy da kuma Marigayi Alhassan Sa’id Jos.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Faɗi Kalamai Masu Jan Hankali Game da Rasuwar Sheikh Giro Argungu, Ya Miƙa Ta'aziyya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dr. Dutsen Tanshi ya ce shekaru 25 da su ka wuce, ya maida martani mai zafi ga Gero Argungu, wanda shi kan shi ya fahimci ya yi tsanani.

Sheikh Abubakar Giro Argungu ina yi masa zaton iyakar fahimtarsa yake yi, domin Allah yake yi.
Meyasa na maidawa Abubakar Giro Argungu raddi mai zafi, wallahi abin da kungiyar Izala ta nan Bauchi ta saba yi, shi su ka yi.

- Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi

Izala ta hada Dutsen Tanshi da Giro Argungu

Me su ka saba? Hada ni da malamai, duk wanni malami da ya shahara idan ya zo Bauchi, sai sun hada ni da shi.

Ya faru a kan Dr. Alhassan Sa’id Jos, abokin karatu na ne, mun yi jami’ar Bayero da shi, tare mu ka tafi Madina.

Kara karanta wannan

Giro Argungu: Atiku Abubakar Ya Mika Sakon Ta'aziyyarsa Ga Iyalan Malamin

A bidiyon da Legit ta saurara, an ji Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya na tuhumar wasu malamai da jefa masa munanan kalamai a bakinsa.

Irin wadannan miyagun kalamai Marigayi Giro Argungu ya hau kai, a sanadiyyar haka kuma Dutsen Tanshi ya yi masa raddi da ya taba shi.

Raddin Dutsen Tanshi ga Giro Argungu

Da malamin ya aikawa shehin fai-fen raddinsa a Argungu, sauraronsa yake da wuya shi kuma sai ya gane kuskurensa, daga nan sai aka sasanta.

Yayin da ya zo garin Darazo bayan shekaru, sai Giro Argungu ya fadawa duniya yadda aka hada shi fada da Idris Dr. Dutsen Tanshi a Bauchi.

Har malamin kungiyar Izalar ya rasu, ya na burin zuwa majalisin Dutsen Tanshi, ya shaidawa Bashir Argungu zai zo masallacinsa a Bauchi.

Kafin malamin ya gabatar da karatu a majalisin kamar yadda ya yi niyya, sai aka samu labarin rasuwarsa wanda ta girgiza musulmai sosai.

Kamar dai Bola Tinubu, Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar sun nuna damuwarsu a kan irin babban rashi da aka yi na malamin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel