“Nigeria Za Ta Murkushe ’Yan Ta’adda Idan Ta Samu Tallafi Daga EU” Inji Ministan Tinubu

“Nigeria Za Ta Murkushe ’Yan Ta’adda Idan Ta Samu Tallafi Daga EU” Inji Ministan Tinubu

  • Ministan tsaro, Mohammed Badaru, ya yi kira ga kungiyar tarayyar Turai da ta tallafawa Nigeria a yaki da matsalar rashin tsaro
  • Mohammed Badaru, ya nuna damuwa kan yadda kasashen Africa ke fama da rashin tsaro a yayin da kuma suke fama da talauci
  • Ministan ya jaddada cewa, karkatar da wani kaso na tallafin da EU ke ware wa rikicin Ukraine zai iya taimakawa yaki da ta'addanci a Nigeria

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bukaci karin tallafi daga kungiyar tarayyar Turai (EU) domin magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta.

Gwamnati na neman tallafin tarayyar Turai
Gwamnatin Najeriya ta nemi kungiyar tarayyar Turai ta tallafa mata a yaki da ta'addanci. Hoto: @EUinNigeria
Asali: Twitter

Najeriya ta nemi tallafin tarayyar Turai

Ministan tsaro, Mohammed Badaru ne ya yi wannan roko a wani taro wanda cibiyar yaki da ta'addanci ta kasa (NCTC) tare da hadin gwiwar EU suka shirya a jiya Laraba.

Kara karanta wannan

Matar ɗan Sarkin Ingila, Harry ta ji dadin Najeriya, ta ce ta samu gida

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohammed Badaru, ya nuna takaici kan yadda kasashen Africa da dama ke fama da matsalar rashin tsaro a yayin da kuma suke cikin matsanancin talauci, in ji rahoton The Punch.

Badaru ya jaddada cewa, karkatar da wani kaso na tallafin da ake ware wa rikicin Ukraine zai iya taimakawa kokarin yaki da ta'addanci a nahiyar Africa.

Matsalalin tsaro da ke addabar Najeriya

Ministan ya zayyana matsalolin tsaro na Nigeria da suka hada da ta'addanci, 'yan fashi da masu garkuwa da mutane, inda ya bukaci kungiyar EU da ta taimaka wajen kawo karshen su.

Jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa babban sakataren ma’aikatar tsaro, Dr Ibrahim Kana, ne ya wakilci Badaru a taron, kuma ya ce rashin tsaro a kasa daya na shafar sauran kasashe.

Ya bayyana damuwa kan cewa ba a damuwa da tsaro a Afirka idan aka kwatanta da tashe-tashen hankula a wasu sassan duniya, duk da bukatar agajin gaggawa da nahiyar ke nema.

Kara karanta wannan

"Sun lalata komai": Tsohon shugaban kasa ya koka yadda aka ruguza ayyukansa

An ta da bam a masallaci a Nigeria

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano sun ce an yi amfani da bam ne wajen kona mutane yayin da suke tsaka da yin sallar asubah a garin Gezawa.

Zuwa yanzu dai adadin mutane da suka mutu a wannan harin ya kai takwas, yayin da kusan mutum 40 ke kwance a gadon asibiti.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel