Tinubu Ya Buƙaci Kasashen ECOWAS Su Haɗa Gwiwa Don Murƙushe Matsalar Tsaro a Afrika ta Yamma

Tinubu Ya Buƙaci Kasashen ECOWAS Su Haɗa Gwiwa Don Murƙushe Matsalar Tsaro a Afrika ta Yamma

  • Shugaba Tinubu ya ce dole ne a samu haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen yammacin Afrika don magance matsalolin tsaro
  • Ya bayyana hakan ne a wajen taron ECOWAS, jim kaɗan bayan zaɓarsa a matsayin shugaban ƙungiyar
  • Tinubu ya kuma bayyana cewa ECOWAS ba za ta lamunci juyin mulki da sojoji ke yi a wasu daga ƙasashen na Afrika ta Yamma ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Guinea-Bissau - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce akwai ɓukatar a ɗauki matakan gaggawa domin daƙile barazanar 'yan ta'adda da ake fama da ita a yankin Afirka ta Yamma, wanda ya ce ya yi ƙamari da yawa.

Ya bayyana hakan ne a ƙasar Guinea, jim kaɗan bayan zaɓarsa da aka yi matsayin shugaban ƙungiyar ECOWAS.

An zaɓi Tinubun ne a wajen taron ƙungiyar ta ECOWAS na 63, wacce ta ke da ƙasashe 16 a matsayin mambobinta, kamar yadda PM News ta wallafa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Cikin Dare a Arewacin Najeriya, Rayukan Mutane Da Yawa Sun Salwanta

Tinubu ya ce dole kasashen ECOWAS su hada gwiwa don tunkarar matsalar tsaro
Tinubu ya ce kasashen ECOWAS za su hada gwiwa don yakar matsalar tsaro. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Tinubu ya nemi ƙasashen ECOWAS su haɗa gwiwa

Mai magana da yawun Shugaba Tinubu Dele Alake, ya ce shugaban ya bayyana cewa matsalar tsaro na ɗaƙile ci gaban ƙasashen Yammacin Afrika.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A dalilin hakan ne Tinubu ya yi kira ga mambobin ƙasashen na ECOWAS, da su zo a haɗa gwiwa wajen ganin an tabbatar da mafarkin ƙungiyar na samar da zaman lafiya da ci gaba a yankin.

Tinubu ya ƙara da cewa idan babu zaman lafiya a yankin, babu yadda za a yi a samu ci gaba.

A cewarsa:

"A dangane da haka, dole ne mu ci gaba da jajircewa wajen yin amfani da dukkan tsare-tsaren da muke da su don magance matsalar rashin tsaro."

Tinubu ya ce 'yan ta'adda ba sa banbancewa tsakanin ƙasa da ƙasa

Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa ƙasashen ECOWAS na da tsare-tsare daban-daban na tsaro, waɗanda suka shafi ɓangarori da dama, irinsu amfani da ƙarfin soji ko kuma amfani da hanyoyi na diflomasiyya.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku Ya Yi Wa Shugaba Tinubu Tonon Silili Kan Dalilin Da Ya Sanya Yake Nade-Naden Mukamai

Ya ce a ƙarƙashin shugabancinsa, zai yi ƙoƙarin ganin an haɗe waɗannan matakai wuri guda don cimma abinda ake buƙata.

Tinubu ya ce dole ƙasashen za su yi aiki na haɗin gwiwa tunda suma 'yan ta'addan ba sa banbance inda suke kai hare-harensu.

Jaridar Leadership ta zaƙulo a cikin bayanin na Tinubu inda yake bayyana cewa ƙasashen na ECOWAS ba za su lamunci juyin mulki da sojoji ke yi a ƙasashen Afrika ba.

Ya ce duk da dimokuraɗiyya ta na da wahala sosai wajen gudanarwa, ita ce ta fi da cewa da al'ummar ƙasashen na Afrika.

El-Rufai ya yi magana kan yadda Tinubu ke gudanar da mulki

Legit.ng ta kawo muku rahoto cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana cewa yadda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke gudanar da mulkinsa ya yi daidai.

Ya bayyana hakan ne a wajen taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar Farfesa Ishaq Akintola a birnin Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel