Majalisa ta yi Alkawarin Kawo Karshen Matsalar Fetur Kwanan Nan
- Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, ya bayar da tabbacin kawo karshen matsalar karancin man fetur a Najeriya nan gaba kadan
- Ya ce bangaren majalisa yana aiki babu gajiyawa wajen ganin an magance dogayen layuka a gidajen mai da tsadarsa a kasar nan
- Daga hanyoyin da dan majalisar ya ce za a bi wajen magance matsalar akwai shigo da karin yan kasuwa masu zaman kansu su gina matatun mai
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja-Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, ya bai wa yan Najeriya tabbacin cewa wahalar man fetur da suke fuskanta za ta zama tarihi nan ba da dadewa ba.
Ya bayar da tabbacin ne ranar Juma’a a wata ganawa da menama labarai a gefen taro kan fasahar man fetur a Houston dake jihar Texas ta Amurka, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
Ya ce bangaren majalisa yana aiki babu gajiyawa wajen ganin an magance dogayen layuka a gidajen mai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ya za a magance matsalar mai?
A cewar shugaban majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, suna shirin shigo da karin bangarori masu zaman kansu domin gina sababbin matatun mai.
A kalamansa:
“Bayan kokarin bai wa sababbin matatu izinin aiki, gwamnatin tarayya da majalisar dattawa suna aiki domin ganin wadanda ake …
Bamidele ya kara da cewa majalisar dattawa ta samu tabbacin daga kamfanin mai na Najeriya NNPCL, cewa matatunsa guda biyu na Warri da Port Harcourt za su fara aiki kafin karshen shekarar 2024, The Guardian ta ruwaito.
Alkawarin shugaban majalisar na zuwa a lokacin da yan Najeriya ke neman saukin matsalar mai da suke ciki.
Wani Muhammad dake zaune a Kano ya bayyana cewa kawai suna kallon gwamnati ne, amma bata nema musu sauki.
Shi ma Aminu Abdullahi, ya bayyana cewa ya kasa shawara kan ya ajiye abun hawansa ko ya ci gaba da lallabawa saboda wahalar samun mai.
Da yawa na yiwa gwamnatin kallon tana alkawari ne amma bata cikawa
Litar mai ya haura N900
Mun ruwaito muku a baya cewa matsanancin karancin man fetur a Najeriya ya jawo farashinsa ya kara tashi.
Yanzu haka litar mai ya haura N900 zuwa N1000 a wasu sassan kasar nan, ciki har da jihar Sokoto inda lamarin ya tabarbare kwarai da gaske.
Asali: Legit.ng