Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai Kalu Ya Sha Alwashin Duba Batun Ƙarin Kuɗin Wuta

Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai Kalu Ya Sha Alwashin Duba Batun Ƙarin Kuɗin Wuta

  • Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu ya ce ƴan majalisa za su waiwayi batun ƙarin kuɗin wutar lantarki da gwamnati ta yi
  • Gwamnatin tarayya ce ta bayyana ƙarin kuɗin ga kwastomomi da ke shan wuta a layin A da B
  • Ƴan Najeriya na ganin ƙarin bai dace ba, musamman idan aka yi la'akari da matsin da ake fama da shi a yanzu

Umuahia, Abia- Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya kwantarwa da ƴan Najeriya hankali kan batun ƙarin farashin wutar lantarki da gwamnatin tarayya ta yi.

Ben Kalu ya ce ƴan majalisar sun ƙudiri aniyar tafka muhawara kan ko ya kamata a yi ƙarin kuɗin wutar ko a'a.

Majalisar wakilan za ta waiwayi karin kudin wutar da gwamnati ta yi idan sun dawo zama a cikin watan nan
Benjamin Kalu ya ce ba za su bar 'yan Najeriya su sha wahala ba. Hoto: @OfficialBenKalu
Asali: Twitter

Jaridar Tribune ta ruwaito dan majalisar ya bayyana haka ne a ranar Litinin ta cikin shirin rediyo a birnin Umuahia a jihar Abia.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki kan dan majalisa har cikin gida a jihar Arewa

Majalisa za ta duba tashin kudin lantarki

A cewar mai magana da yawun Kalu, Levinus Nwabughiogi, ɗan majalisar na amsa tambayar wani mai sauraro da ya yi kiran waya cikin shirin yana tambayar matsayar majalisa kan ƙarin kuɗin wutar kamar yadda Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalu ya ce:

"Gama-garin matsala ce. Ina cikin hutu, amma daga abin da ke damina akwai takardar da shugaban masu rinjaye na majalisa ya aiko min yana neman mu shiga batun samar da hasken wutar lantarki ga asibitin koyarwa na garin Ibadan." "An yanke musu (asibitin koyarwa na Ibadan) wuta saboda karin kuɗin wutar da aka yi kuma ba su da kuɗin biya.

Benjamin Kalu ya ce ba za su bar 'yan Najeriya su sha wahala ba sakamakon karin kudin wutar.

Gwamnati ta sanar da karin kudin wuta

A watan Afrilu ne, Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu ya sanar da karin kudin wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Karin kudin lantarki: Sanatan APC ya soki gwamnatin Bola Tinubu

Daga dalilan da ya bayar na karin kudin, ya ce gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin wutar da ta ke biya a baya ba.

Ba kowa karin kudin ya shafa ba

Hukumar kula da rarraba hasken wutar lantarki, NERC ta ce unguwanni 481 a fadin kasar nan ne ƙarin kuɗin ya shafa.

An rahoto cewa unguwannin na karkashin tsarin band A da B, saboda suna sahun farko da na biyu wajen morar wutar lantarkin.

Hukumar ta ce 'yan Najeriya za su iya ziyartar shafukansu domin sanin inda suka fada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel