Miji ya yiwa matarshi karyar ya mutu saboda tambayarshi kudi da take

Miji ya yiwa matarshi karyar ya mutu saboda tambayarshi kudi da take

Wasu lokutan mutane na ganin cewa mutuwa ita kadai ce mafita idan suka shiga wani matsi na rayuwa. Kamar dai yadda Danny Gonzalez dake birnin Honduras yayi tunani

Danny na zaune a kasar Amurka na tsawon wani lokaci, kwatsam sai jin kiran waya yayi daga matarshi cikin fada da masifa.

Wannan masifa ta matar tashi tayi masa yawa hakan ya sanya ya fara neman hanyar samawa kanshi saurki daga wannan soyayyar wahala da yake yi da matarsa. Tilas ta sanya Danny kirkiro mutuwar karya.

Danny ya sanya an dauki hotonsa yana kwance tamkar ya mutu, cikin hancinsa an sanya audiga, sannan jikinsa sanye da likkafani.

Haka kuma a wani hoton da ya sanya an nuna akwatin gawar da aka dauko shi dauke da fulawoyi, inda ya bayyana cewa cutar daji da asma ce tayi sanadiyyar mutuwarsa.

KU KARANTA: Mata daya ta ishi mutum ya kari rayuwarshi a duniya - Sheikh Al-Qarni

Danny ya aika duka wadannan hotuna ga matarshi dake birnin Honduras. Kafafen yada labarai na garin suka dauki labarin suka dinga yadawa.

Sai dai daga baya da aka gabatar da bincike sun gano cewa Gonzalez na nan da ranshi bai mutu ba.

“Mata ta na kirana kowanne sati ta ce mini na tura mata kudi,” cewar Gonzalez a lokacin da yake bayyana dalilinshi na mutuwar karya. “Na aika mata da wayoyin salula guda shida, amma kullum sai ta kirani tace mini an sace.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel