Ke duniya! Matsafa na kutse a makabartu a wani yankin jihar Kano

Ke duniya! Matsafa na kutse a makabartu a wani yankin jihar Kano

- Al'ummar yankin Rimin Kebe na iya Kano na cikin tashin hankula

- Tashin hankulan ya bullo ne sakamakon kutsen da matsafa ke yi a makabartar yankin

- Sakataren kwamitin kula da makabartar ya ce, matsafan na aika-aikar ne cikin dare lokacin da suka tabbatar sawu ya dauke

Jama'ar yankin Rimin Kebe na jihar Kano sun mika akan kutsen da wasu batagari da suke zargin matsafa ne ke yi a makabartunsu.

Jama'ar yankin sun ce, miyagun mutanen kan shiga makabartun ne cikin dare don cimma miyagun burikansu wadanda ke da nasaba da tsafe-tsafe.

Sakataren kwamitin kula da makabartar, Abdullahi Yusuf, ya shaidawa BBC irin tashin hankulan da suke yin ido biyu dasu wadanda suka hada da tarkacen kayan tsafi a makabartar.

KU KARANTA: Tsananin yunwa ta sanya 'yan ta'addan Boko Haram mika kansu ga rundunar sojin Najeriya

Yusuf ya danganta kutsen da ake yi da rashin katangar da makabartar bata da ita.

"A mako na farko, mun ga kwarya cikin kabari rufe da ganyayyaki da allurai sun fi dubu. A mako na biyu ma abinda muka gani kenan. A mako na uku kuwa, koko muka gani na tukunya lullube da likkafani an rubuta sunaye a jikinsa. A mako na hudu kuwa mukamukin sa muka gani anyi rubutu jikinsa tare da nannadesa da likkafani." In ji Yusuf.

Yusuf yace duk kokarin ganin kawo karshen lamarin ya ci tura saboda matsafan shammatarsu suke yi. A don haka ne yake kira ga gwamnatin jihar Kano da ta kai dauki.

Mai magana da yawun gwamnatin jihar Kano, Yusuf Tarauni, ya ce, gwamnatin jihar ta ce zata hukunta mutanen da ake zargi da aika-aikar domin hakan ya zama izini ga masu muguwar dabi'ar.

Ya ce, "Daga cikin matakan da gwamnatin jihar zata dauka don dakile mugun aikin ya hada da katange makabartar tare da samar da masu gadi don tabbatar da tsaro."

Ya kara da yin kira ga jama'a da su taimakawa kokarin gwamnati ta hanyar bada gudummawarsu ta hanyar kai rahoton wadanda ba a yadda da take-takensu ba a yankin ga hukuma mafi kusa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel