Zabe: An gano asirin da magauta su ka yiwa El-Rufa’I asiri a Kaduna

Zabe: An gano asirin da magauta su ka yiwa El-Rufa’I asiri a Kaduna

An gano wata gora da ke dauke da wasu kayan kulumbuto da wasu rubutun surkulle da aka yi da ajami a wasu makabartu a unguwannin Sabon Kawo da Unguwar Dosa.

Daga cikin rubutun surkullen da aka yi a jikin wata gorar duma an rubuta sunan gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Ruf’ai da Haruna Aliyi Chakis a cikin likkafani a kulle sannan aka binne a makabartar.

Ana zargin wasu magauta gwamnan da shirya ma sa wannan kulumbuto domin ya mutu kafin a gudanar da zaben gwamnoni na jiya ko kuma ya fadi.

A zaben da aka gudanar jiya a Kaduna, kun ji cewar a sakamakon zaben jihar Kaduna ya nuna cewa ‘dan takarar PDP Honarabul Muhammad Isah Ashiru Kudan ya doke jam’iyyar APC a akwatin sa da ke Mazabar sa a cikin Kudan. APC ta samu kuri’a 33 ne yayin da PDP ta samu 284.

Zabe: An gano asirin da magauta su ka yiwa El-Rufa’I asiri a Kaduna
An gano asirin da magauta su ka yiwa El-Rufa’I asiri a Kaduna
Asali: Twitter

Malamin zaben da yayi aiki a rumfa ta 007 da ke cikin Unguwar Kofar Fada a karamar hukumar ta Kudan ya bayyana wannan. Shi ma dai ‘dan takarar na PDP ya sha kashi hannun gwamna Nasir El-Rufai a ta sa mazabar a Kaduna.

DUBA WANNAN: Kai-tsaye: Yadda zaben gwamnoni da 'yan majalisun jiha ke gudana a Sokoto, JIgawa da Kebbi

Tuni dai sanarwar da aka fitar ta nuna cewar gwamna El-Rufa'i ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar Kaduna da banbancin kuri'u ma su yawa.

An fafata a takarar gwamnan jihar Kaduna ne tsakanin gwamna mai ci, El-Rufa'i, da babban abokin hamayyar sa a jam'iyyar PDP, Isah Ashiru Kudan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel