Boko Haram Sun Shigo Shekarar 2024 da Ta’addanci, Sun Yi Kashe Kashe a Kauyukan Chibok

Boko Haram Sun Shigo Shekarar 2024 da Ta’addanci, Sun Yi Kashe Kashe a Kauyukan Chibok

  • ‘Yan Boko Haram sun yi ta’addancin farko a shekarar 2024 a wasu kauyukan da ke karkashi yankin Chibok
  • A ranar Litinin aka samu labari wasu da ake tunanin ‘yan ta’adda ne, sun buda wuta sun hallaka mutane a Borno
  • ‘Yan ta’addan sun zo dauke da kayan sojoji su ka kashe mutane 12, kuma har sun dauke wani Bawan Allah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Borno - Wasu da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne a kayan sojoji, sun kashe Bayin Allah a wasu kauyukan jihar Borno.

Rahoton Daily Trust ne ya tabbatar da cewa an kashe mutane 12 a Gatamarwa da Tsiha a karamar hukumar Chibok da ke Borno.

Boko Haram
Boko Haram sun kashe mutane a Chibok Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Boko Haram da kayan sojoji?

Kara karanta wannan

NNPC na rikici da ‘yan kasuwa, ana zancen litar fetur ta haura N1200 a kasuwa

‘Yan ta’addan da ake tunani Boko Haram ne sun dauke wani mutumi a harin da aka kai makonni bayan sun datse kan jama'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kusan wannan ne harin farko da aka samu labari bayan an shiga shekarar 2024 inda Bola Tinubu ya yi alkawarin samar da tsaro.

A jawabin shiga 2024, shugaba Bola Tinubu ya yi bayanin kokarin da yake yi a boye.

'Yan sanda sun ce an kai hari a Borno

Kakakin rundunar ‘yan sandan reshen jihar Borno, ASP Nahum Daso Kenneth, ya tabbatar da labarin wannan mummunan hari jiya.

ASP Nahum Daso Kenneth ya ce sun samu gawawwakin mutane 12 da aka hallaka.

Jami’in ‘dan sandan ya ce ‘yan ta’addan sun buda wuta, su kayi ta harbin jama’a, yanzu an samu mutane biyu da ke dauke da rauni.

‘Yan ta’addan sun auka kauyen Gatamarwa da kimanin karfe 5:00 na yamma, ana tsakiyar bikin murnar shiga sabuwar shekara.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba zai yi wa ma’aikatan Kano karin kudi saboda cire tallafin man fetur

Za a kawo karshen Boko Haram

Kwamishinan ‘yan sandan da sauran shugabannin jami’an tsaro sun yi alkawarin yin bincike domin bankado asirin ‘yan ta’addan.

Jami'an tsaro sun ce 'yan ta'addan sun shigo Chibok ne a babura da Hilux. Punch ta fitar da makamancin rahoton a makon nan.

'Yan ta'addan Boko Haram a Chibok

Rahoto ya nuna duka-duka ba a wuce makonni biyu da ‘yan Boko Haram su ka kai wani makamancin wannan hari a Chibok ba.

A lokacin an kashe mutane biyu, sannan aka saci kayan abinci kuma aka kona gidaje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel