Shanu 50 Sun Sake Yin Mutuwar Ban Mamaki a Wani Gari a Ondo

Shanu 50 Sun Sake Yin Mutuwar Ban Mamaki a Wani Gari a Ondo

- Kimanin shanu 50 sun yi mutuwan ban mamaki a karamar hukumar Akoko a jihar Ondo

- Wani mazaunin garin, Fela Castro ya ce wata majiya ta fada masa cewa guba da shanun suka ci ya kashe su

- Castro ya gargadi mutane da su yi taka tsantsan kada a sayar musu da naman shanun mai guba don za su iya mutuwa

A kalla shanu 50 ne suka mutu a wani yanayi mai daure kai a Akungba-Akoko, a karamar hukumar Akoko na jihar Ondo, Vanguard ta ruwaito.

An gano cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin da yamma a yankin Ibaka na garin.

DUBA WANNAN: An Sake Cinnawa Sufetan 'Yan Sanda Wuta Da Ransa a Akwa Ibom

Shanu 50 Sun Sake Yin Mutuwar Ban Mamaki a Wani Gari a Ondo
Shanu 50 Sun Sake Yin Mutuwar Ban Mamaki a Wani Gari a Ondo. Hoto: Vanguardngrnews
Asali: UGC

Wani mazaunin Akungba, Oshk Fela Castro ya shaidawa SaharaReporters cewa shanun sun mutu ne bayan cin wani abu da ake zargin guba ne.

Ya shawarci mazauna garin su guji sayar nama mai araha domin yana zargin wasu masu sayar da nama marasa gaskiya za su iya sayar da naman shanun da suka mutu.

"Bayanin da na samu shine shanun sun mutu bayan cin wani abu da ake zargin guba ne. Kuma an fada min cewa duk wanda ya ci naman zai iya mutuwa saboda gubar. Shanun sun fara rubewa bayan minti 30 bayan mai su ya gano sun ci guba.

KU KARANTA: Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji

"Don Allah ku fadawa makwabta da abokanku su yi takatsantsan wurin siyan nama. Ina son jami'an tsaro su tabbatar ba a siyar da naman wadannan shanun da suka mutu ba," in ji shi.

A 2019, an ruwaito cewa tsawa ta kashe kimanin shanu 36 a Ijare, karamar hukumar Ifedore a jihar Ondo.

Duk da ikirarin da wasu mazauna garin suka yi na cewa tsafi ne ya kashe shanun saboda Fulani sun keta cikin wurin bautar masu addinin gargajiya, yan sanda sun ce tsawa ce kawai.

A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.

Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel