Mulkin Tinubu Ya Dara Shekaru 16 a PDP ta Fuskar Tsaro, Hadimin Tinubu

Mulkin Tinubu Ya Dara Shekaru 16 a PDP ta Fuskar Tsaro, Hadimin Tinubu

  • Jam'iyya mai mulki ta APC ta musanta zargin cewa shugaba Bola Tinubu na kokarin mayar da kasar tsarin jam'iyya daya tal
  • Mashawarcin shugaba kasa na musamman kan kafafen yada labarai, Bayo Onanuga ne ya mayar da martani a sanarwar da ya fitar
  • Ya ce kamata ya yi APC ta mayar da hankali wajen warware matsalolin da suka dabibaye ta a halin yanzu ba wai sa mata ido ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Fadar shugaban kasa ta yi martani ga jam'iyyar PDP kan sukar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na kokarin mayar da kasar tsarin jam'iyya daya.

Kara karanta wannan

Kasar Yarbawa: Kotu ta rufe masu fafutukar raba Najeriya bisa zargin cin amana

Mashawarcin shugaban kasar na musamman kan kafafen yada labarai, Bayo Onanuga ya ce an samu ci gaba sosai ta fannin tsaro idan aka kwatanta da shekaru 16 da PDP ta yi tana jagorantar kasar nan.

Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Fadar shugaban kasa ta yi martani ga PDP ka matsalar tsaro Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya ce baya ga kyankyashe boko haram ƙarƙashin mulkin PDP a shekarar 2009,ya zargi gwamnatin da wawashe kudin jama'a da sunan samawa jami'an tsaro kayan aiki amma ba abin da aka yi, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Onanuga, an samu raguwar sace-sacen jama'a a yan kwanakin nan, kuma sojojin kasar nan sun ceto da dama daga wadanda aka yi garkuwa da su a baya.

A kalamansa:

"Ba kamar gwamnatin PDP da ta shafe shekaru 16 ba, gwamnatin Tinubu ta dauki gabarar magance matsalolin kasar nan."

"Ana samun warwarewar matsin tattalin arziki," Onanuga

Kara karanta wannan

"Ɗaurin shekaru 5": EFCC ta ja kunnen gwamnan APC da masu kawo cikas kan Yahaya Bello

Mashawarcin shugaban kasar ya kuma bayyana yadda gwamnati ke kokarin magance matsalar tattalin arziki.

Ya ce a yanzu haka, gwamnati ta dauki matakan farfado da darajar Naira, kamar yadda Tribune Online ta wallafa.

Onanuga ya kara da cewa farfadowar darajar Naira da kusan kaso 50% ya sa bankin bayar da lamuni na duniya (IMF) ya daga hasashen karuwar tattalin arzikin Najeriya zuwa kaso 3.3% daga 2.9%.

Ya bayyana gina manyan titunan Badagry-Sokoto da na Legas-Kalaba a matsayin manya-manyan ayyukan raya kasa.

Bayo Onanuga ya shawarci PDP ta warware matsalolin cikin gida da suka kanainayeta, maimakon sanyawa APC ido.

PDP ta zargi APC da katsalandan

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta zargi jam'iyya mai mulki ta APC da kawo rudani cikin jam'iyyun adawa.

Mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Iliya Damagum ne ya yi zargin, inda ya ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta jefa 'yan Najeriya cikin halin Ni 'ya su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel