A kula: Gwamnatin wata jihar Arewa ta gano bullar nama mai guba a Najeriya
Gwamnatin jihar Neja dake a shiyyar Arewacin Najeriya ta tsakiya ta ce jami'an ta sun gano kwararar nama mai guba a kasuwannin jihar sakamakon anfani da wasu magunguna da makiyaya da mahautan jihar keyi ga dabbobin su.
Kamar yadda muka samu, gwamnatin kuma ta ce magungunan na dauke da sinadarin guba da kan iya yin lahani ga lafiyar 'yan adam.
KU KARANTA: Sojin Najeriya sun yi wa Shekau mummunar ta'asa
Wannan dai mun samu haka ne a ta bakin kwamishin ayyukan gona na bangaren kiwon dabbobi da kifi a jihar, Zakari Bawa yayin da yake yiwa manema labarai jawabi jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswar jihar da ya gudana.
Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa Kwamishin yace yana anfani da wannan damar wajen kira ga dukkan al'ummar jihar da suyi taka tsan-tsan wajen siyen naman da za su ci sannan kuma yayi alkawarin cewa gwamnatin su zata dauki mataki domin dakile mugunyar dabi'ar.
A wani labarin kuma, Labarin da muka samu daga majiyar mu ta Blue Print, ya na nuni ne da cewa jim kadan bayan saukar jirgin dake dauke da dan takarar shugaban kasar Najeriya na jam'iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, jami'an tsaro suka shiga bincikar sa.
Tsohon kakakin jam'iyyar na APC, Mista Timi Frank wanda kuma ke cikin tawagar tsohon shugaban kasar shine ya bayyanawa majiyar ta mu hakan a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng