Hattara jama'a: Gwamnati ta gano bullar nama mai guba a arewacin Najeriya
Gwamnatin jihar Neja dake a shiyyar Arewacin Najeriya ta tsakiya ta ce jami'an ta sun gano kwararar nama mai guba a kasuwannin jihar sakamakon anfani da wasu magunguna da makiyaya da mahautan jihar keyi ga dabbobin su.
A cewar gwamnatin kuma, magungunan na dauke da sinadarin guba da kan iya yin lahani ga lafiyar 'yan adam.
KU KARANTA: An zargi wasu gwamnoni 3 da shiryawa Buhari makarkashiya
Wannan dai mun samu haka ne a ta bakin kwamishin ayyukan gona na bangaren kiwon dabbobi da kifi a jihar, Zakari Bawa yayin da yake yiwa manema labarai jawabi jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswar jihar da ya gudana.
Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa Kwamishin yace yana anfani da wannan damar wajen kira ga dukkan al'ummar jihar da suyi taka tsan-tsan wajen siyen naman da za su ci sannan kuma yayi alkawarin cewa gwamnatin su zata dauki mataki domin dakile mugunyar dabi'ar.
A wani labarin kuma, Wata tawagar dalibai daga jami'ar Ahmadu Bello University (ABU), Zaria - jihar Kaduna ta zama zakara a wajen wata muhimmiyar gasa ta baje kolin fasahohi karo na 7 da cibiyar habaka ilimin lissafi ta kasa ke shiryawa duk shekara watau Nigeria Universities Computer Programming Contest (NUCPC).
Mun samu cewa tawagar dalibai daga jami'ar fasaha ta garin Akure ce ta zo na biyu a gasar yayin da kuma jami'ar jihar Ebonyi ta zo na uku duk dai a gasar wadda a gudanar a garin Abuja, babban birnin tarayya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng