An Rage Mugun Iri Bayan Hallaka Kasurgumin Ɗan Ta'adda da 'Yan Bindiga Suka Yi Fada

An Rage Mugun Iri Bayan Hallaka Kasurgumin Ɗan Ta'adda da 'Yan Bindiga Suka Yi Fada

  • An rincabe da fada tsakanin manyan hatsabiban 'yan bindiga da suka addabi jihohin Zamfara da kuma Katsina a Arewacin Najeriya
  • Kasurgumin ɗan bindiga, Sani Dangote ya gamu da ajalinsa bayan artabu da tsagin Kachalla Dankarami a karamar hukumar Zurmi a jihar
  • Lamarin ya faru ne bayan kwanton ɓauna da Kachalla ya yi kan Dangote inda ya hallaka shi da 'yan uwansa guda biyu kan zargin satar shanu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Kasurgumin dan ta'adda da ya addabi jihohin Zamfara da Katsina ya rasa ransa bayan artabu tsakaninsa da wani tsagi na 'yan bindiga.

Dan ta'addan mai suna Sani Dangote ya rasa ransa ne yayin artabu da gungun 'yan bindiga da ke karkashin jagorancin Kachalla Dankarami.

Kara karanta wannan

Rikici da malamin addini: Dr Idris Dutsen Tanshi ya dawo Bauchi bayan gudun hijirar kwanaki

Hatsabibin ɗan bindiga ya mutu yayin artabu da abokan gaba a Zamfara
An hallaka kasurgumin dan ta'adda, Sani Dangote yayin artabu da Kachalla Dankarami a Zamfara. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Twitter

Zamfara: Yadda Dangote da yaransa suka mutu

Dangote da manyan yaransa sun gamu ajalinsu ne a karshen mako da kannensa guda biyu, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne a Dumburum a karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara yayin da Dankarami ya yi kwanton bauna kan Dangote.

Wata majiya daga jami'an tsaro ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne bayan zargin Dangote da satar shanu da tumaki a yankin.

Majiyar ta ce an fara artabu ne tun misalin karfe biyu na rana har zuwa karfe shida shida na yamma inda 'yan bindiga da dama suka mutu.

Dangote v Kachalla: Musabbabin fadan 'yan ta'adda

"Dankarami ya sace shanun Sani Dangote, wannan shi ne musabbabin fadan a tsakaninsu, Dankarami ya hallaka Dangote da kannensa biyu."

Kara karanta wannan

"Za mu waiwayi bidiyon dala": Abba ya magantu kan shekara 8 na mulkin Ganduje a Kano

"A lokacin Dankarami ya na Rukudawa inda ya samu labarin rikicin yayin da ya zo Dumburum ya sami labarin suna shirin kai masa farmaki."
"Shi kuma sai ya yi maza ya kai musu farmaki inda ya hallaka Dangote da 'yan uwansa guda biyu, Lamo Balewa da Usman Yellow."

- Cewar majiyar

Channels TV ta ruwaito cewa shi ma Dankarami ya samu raunuka a jikinsa yayin da wasu daga cikin yaransa suka mutu.

An bayyana gaskiya kan mutuwar Dogo Giɗe

A wani labarin, kun ji cewa bayan yada jita-jitar mutuwar hatsabibin ɗan bindiga, Dogo Giɗe, an bayyana gaskiya kan lamarin.

Legit Hausa ta yi bincike mai zurfi inda ta gano babu kamshin gaskiya kan mutuwar tashi jihar Sokoto wanda har yanzu bai tabbata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel