Sadiya da Betta: Yadda Gwamnati da Bankaɗo Makudan Kuɗin da Aka Sace a Ma'aikatar Jin Ƙai

Sadiya da Betta: Yadda Gwamnati da Bankaɗo Makudan Kuɗin da Aka Sace a Ma'aikatar Jin Ƙai

Ɗaya daga cikin abubuwan da suka ja hankalin ƴan Najeriya bayan kama aikin ministoci a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu shi ne badaƙalar da aka bankado a ma'aikatar jin ƙai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Dokta Betta Edu, matar da shugaban ƙasa ya ba amanar ma'aikatar jin kai da yaye talauci na ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da hannu a tura wasu kuɗaɗe zuwa asusun kai da kai.

Sadiya da Betta Edu.
Badakatar ma'aijatar jin kai tun daga Sadiya zuwa Betta Edu Hoto: Sadiya Umar Farouq, Dr. Betta Edu
Asali: Twitter

A wannan shafin, Legit Hausa ta tattaro muku muhimman bayanai kan badaƙalar da yanzu haka ake bincike a ma'aikatar jin ƙai tun daga tsohuwar gwamnati.

Abin da ya kamata ku sani game da ma'aikatar jin ƙai

A ranar 21 ga watan Augusta, 2019, tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sanar da ƙirƙiro ma'aikatar jin kai da walwalar al'umma ta tarayya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗe wuta, sun kashe ɗalibin jami'a da wasu bayin Allah a Filato

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya bayyana haka ne a wurin rantsar da sababbin ministocin da ya naɗa waɗanda za su yi aiki a zangon mulkinsa na biyu bayan ya samu nasarar tazarce.

Bayan haka Buhari ya rantsar da Dr. Sadiya Umar Farouq a matsayin ministar ma'aikatar jin ƙai, magance bala'o'i da walwalar al'umma ranar 24 ga watan Augusta, 2019.

Sadiya ta kwashe tsawon shekaru huɗu tana jagorantar ma'aikatar amma tun kafin ta sauka, ƴan Najeriya da dama sun yi kiraye-kirayen a binciki yadda ta kashe kuɗaɗen ma'aikatar.

Bayan Tinubu ya karɓi ragamar mulkin Najeriya, ya canza sunan ma'aikatar zuwa ma'aikar jin kai da yaki da fatara kuma ya naɗa Betta Edu a matsayin minista.

Ayyukan da ma'aikatar ke yi

Wannan ma'aikata tana da matuƙar tasiri a rayuwar ƴan Najeriya domin ita ke da alhakin dukkan harkokin jin kai a sassan kasar nan.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai ƙazamin farmaki hedkwatar ƙaramar hukuma, sun tafka ɓarna

Muhimman ayyukanta sune, samar da tsare-tsaren jin ƙai, kokarin magance ibtila'i da kuma agaza wa waɗanda irin haka ta shafa.

Ma'aikatar ce ke kula da shirye-shiryen walwala da tallafawa mutane. Ɗaya daga cikin shirin da ya fi shahara kuma mutane ke amfana shi ne Npower.

Sannan ma'aikatar ce kula da duk wasu ƙungiyoyin duniya da za su shigo su rabawa mutane kayan jin ƙai musamman duba da taɓarɓarewar tsaro.

Ana zargin Sadiya Farouk ta ci kuɗaɗe

A watan Janairu, 2024, hukumar yaƙi da rashawa EFCC ta gayyaci tsohuwar Ministar jin ƙai, Sadiya Farouq, kan wawure maƙudan kuɗi da suka kai N37bn.

Binciken da EFCC ke ci gaba da yi na zunzurutun kudi har Naira biliyan 37.1 (N37,170,855,753.44), ana zargin jami’an ma’aikatar jin kai karkashin Sadiya suka cinye su.

Sadiya Umar Farouk
EFCC ta fara bincike kan wasu kuɗaɗe da ake zargin Sadiya ya cinye Hoto: Sadiya Umar Farouq
Asali: Twitter

Amma tun farkon fara binciken EFCC, Sadiya Farouk ta fito a shafinta na manhajar X ta musanta hannunta a badaƙalar, in da ta ce a shirye take ta kare kanta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta tsoma baki kan rikicin Iran da Isra'ila

“Ina alfahari da yi wa kasata hidima a matsayin minista a Tarayyar Najeriya, kuma zan kare ayyukana, kula da shirye-shiryen walwala a lokacin wa'adina duk lokacin da buƙatar hakan ta taso," in ji ta.

A watan Satumba, 2020, hukumar ICPC mai yaƙi da rashawa ta ce ta gano wasu maƙudan kuɗi N2.6bn na ciyar da ɗaliban da aka lamushe a ma'aikatar lokacin korona.

Zuwan Betta Edu a mulkin Tinubu

A ranar 21 ga watan Augusta, Dokta Betta Edu ta karbi rantsuwar kama aiki a matsayin ministar jin ƙai da yaƙi da talauci, ta gaji Sadiya Umar Farouq, Channels tv ta ruwaito.

Zuwan Edu wannan ma'aikata ya sa ƴan Najeriya da dama farin ciki da fatan samun sauyi a tsare-tsaren tallafi da haƙƙonn matasan Npower da suka maƙale.

Sabuwar ministar ta ƙara samun karɓuwa yayin da ta sanar da cewa za a ta ci gaba da biyan ma'aikatan shirin Npower na rukunin C.

Kara karanta wannan

Murna yayin da Dala ta karye zuwa kasa da N1,000, Hadimin Buhari ya magantu

Ta kawo sauye-sauye da dama a ɗan lokacin da ta ɗauka a kan kujerar ministar jin ƙai, kama daga sake fasalin Npower, tsare-tsaren kawar da talauci da sauran ayyukan jin ƙai.

Dakatarwa da tuhumar Betta Edu

Bayan ƴan watanni da kama aiki, wata takardar ta fito inda aka ga Betta Edu ta umarci Akanta Janar ta ƙasa ta tura N585m zuwa wani asusun kai da kai.

Wannan lamari dai ya tada ƙura a dukkan sassan Najeriya yayin da aka yi kiraye,-kirayen ga Bola Ahmed Tinubu ya ɗauki matakin da ya dace, rahoton The Cable.

Bayan wasu ƴan kwanaki Shugaba Tinubu ya sanar da dakatar da Edu daga matsayin ministar jin ƙai da yaye talauci, kana ya umarci EFCC ta gudanar da bincike.

Sa'o'i bayan haka, ministar ta garzaya fadar shugaban ƙasa domim ganawa da Tinubu amma aka hana ta ganin shi. Daga nan kuma EFCC ta aike mata da goron gayyata.

Kara karanta wannan

Muna buƙatar bishiya 1 tsakanin gidaje 5 don yaƙar dumamar yanayi inji Anka

Edu ta amsa gayyatar inda jami'an EFCC suka titsiyeta na tsawon awanni kan badaƙalar N585m da ake zargin ta tura asusu. Daga ƙarshe aka sake ta a beli.

Ƙarin bincken da aka yi daga baya

Bayan Edu ta amsa tambayoyi, hukumar EFCC ta ci gaba da bincike kan ayyukan ma'aikatar kuma daga baya ta gano daraktoci da manyan jami'ai da dama masu hannu a badaƙalar.

A makon da ya gabata, BBC ta wallafa rahoton cewa EFCC ta bi diddigin wasu asusun banki 50 kuma ta kwato kuɗi N30bn.

Hukumar ta bayyana cewa kuɗin suna da alaƙa da binciken da take yi kan kes din dakatacciyar ministar jin ƙai, Betta Edu.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai suna, “EFCC Alert,” wanda ke yin cikakken bayani game da wasu manyan ayyukan da hukumar ta yi a watan da ya gabata.

Sanarwan ta bayyana cewa N30bn da aka kwato daga asusun bankunan yanzu haka an sanya su a baitul malin gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Zamfara: Dakarun sojoji sun sheke 'yan ta'adda 12 a wani sabon hari

Edu: Halin da ake ciki yanzu

Duk da ana ci gaba da bincike, gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na ci gaba da wasu tsare-tsare ma'aikatar jin ƙai waɗanda aka dakatar saboda abin da ya faru.

Tun farko, shugaban ƙasa ya dakatar da duk wasu shirye-shiryen da hukumar NSIPA ke gudanarwa na tsawon makwanni shida, a wani bangare na binciken badakalar da ake yi.

Shirye-shiryen da abin ya shafa sun hada da N-Power, tallafin CCT, shirin ba da tallafin kudi, da shirin ciyar da ɗalibai a makarantu.

Amma ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya ce kwamitin da Tinubu ya naɗa kan lamarin ya gama bincike, kuma nan ba da jimawa za a ci gaba da shirye-shiryen.

Kammalawa

A halin yanzun abin da ƴan Najeriya ke dakon su gani shi ne shin Tinubu zai mayar da dakatacciyar ministar kan kujerarta bayan gama bincike ko zai naɗa wata.

An fara samun wasu kungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane suna kira a ƙara bai wa Betta Edu dama ta biyu yayin da wasu ke ganin ma'aikatar na buƙatar mutum mai gaskiya.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya kawo mafita ga yan Najeriya kan ƙoƙarin Tinubu na kawar da ƴan bindiga

Cikar Tinubu shekara 1 a mulki

A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamitin da zai dauki alhakin gudanar da taron bikin cika shekara guda na mulkin Shugaba Tinubu

Taron wanda za a gudanar domin tunawa da ranar 29 ga watan Mayu, 2023, zai waiwayi nasarorin da Tinubu ya samu a shekara daya

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262