'Yan Bindiga Bun Buɗe Wuta, Sun Kashe Ɗalibin Jami'a da Wasu Bayin Allah a Filato

'Yan Bindiga Bun Buɗe Wuta, Sun Kashe Ɗalibin Jami'a da Wasu Bayin Allah a Filato

  • Ƴan bindiga sun halaka mutum uku yayin da suka kai hari kauyen Butura a ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Filato
  • Daga cikin waɗanda maharan suka kashe har da ɗalibin jami'a a Bokkos kuma kisan ya haifar da zanga-zanga daga ƴan uwansa ɗalibai
  • Wannan na zuwa ne bayan kashe wasu mutum uku na daban a kauyuka biyu a ranar Lahadi da ta gabata a kananan hukumomin Bokkos da Mangu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindiga sun kashe akalla mutum uku cikin har da ɗalibin jami'ar Bokkos ranar Alhamis da daddare a jihar Filato.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro, ƴan bindigan sun kashe mutanen ne yayin da suka kai farmaki ƙauyen Butura da ke ƙaramar hukumar Bokkos a jihar.

Kara karanta wannan

Benue: Tashin hankali yayin da ƴan sanda suka ƙwace iko da sakateriyar APC

Gwamna Celeb Mutfwang.
Yan bindiga sun ƙara aikata ta'adi a jihar Filato Hoto: Celeb Mutfwang
Asali: Facebook

'Yan bindiga sun kashe mutane

Wani ɗalibin jami'ar Bokkos wanda ya ambaci sunansa da George Lazarus, ya ce ɗalibin aji biyu da ke karatun kimiyyar na'ura mai kwakwalwa na cikin waɗanda aka kashe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanai sun nuna cewa ƴan bindigar sun kutsa cikin ƙauyen da misalin ƙarfe 9:00 na dare kuma daga zuwa suka buɗe wuta kan mao uwa da wabi.

...Ɗalibai sun fito zanga-zanga

Wasu majiyoyi daga kauyen Butura sun shaida cewa kisan ɗalibin jami'ar ya haddasa zanga-zangar ɗalibai ƴan uwansa a yankin.

Amma dai jami'an rundunar Operation Safe Haven da ke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin sun tarwatsa masu zanga-zangar.

Yayin da aka tuntuɓe shi, mai magana da yawun rundunar Operation Safe Haven, Manjo Samson Zhakom ya ce ba shi da masaniyar kai harin amma zai bincika kafin ya faɗi wani abu.

Kara karanta wannan

"Lamarin ya yi muni" Ƴan bindiga sun kewaye gari guda, sun tafka mummunar ɓarna a Kaduna

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, bai fitar da sanarwa a hukumance ko ƙarin bayani kan lamarin ba, Channels tv ta ruwaito batun.

A ranar Lahadin da ta gabata ma an kai wani hari makamancin wannan kan wasu kauyuƙa biyu a kananan hukumomin Mangu da Bokkos inda aka kashe mutane uku.

Yan sanda sun kwace sakateriyar APC

A wani rahoton kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sanda sun ƙara kwace iko da sakatariyar tsagin APC wanda Kwamared Austin Agede ke jagoranta a jihar Benue.

Rahoto ya nuna cewa tun da farar safiya ƴan sanda suka girke motocin su, suka toshe duk wata hanya ta shiga sakateriyar a Makurɗi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel