Muna Buƙatar Bishiya 1 Tsakanin Gidaje 5 Domin Yaƙar Ɗumamar Yanayi Inji Anka

Muna Buƙatar Bishiya 1 Tsakanin Gidaje 5 Domin Yaƙar Ɗumamar Yanayi Inji Anka

  • Akwai bukatar shuka bishiya aƙalla ɗaya tsakanin gidaje biyar domin gyara iskar da al'umma ke shaƙa da kare muhalli
  • Mai fafutukar kare muhalli a Najeriya, Umar Sale Anka ya shaidawa Legit Hausa buƙatar a gaggauta ɗaukan matakin shuka bishiya domin kare lafiya
  • Wannan na zuwa ne bayan hukumar NIMET ta yi gargaɗin tsananin zafi a wasu jihohin Arewa ka iya jawo shanyewar ɓarin jiki saboda zafi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano, Najeriya– Ƙungiyar rajin kare muhalli ta ƙasa (Nigerian Environmental Society) ta ce har yanzu duniya ba ta kai gaɓar da za a gaza samun yanayi mai kyau ba. Ɗaya daga ƙusoshin ƙungiyar, Umar Saleh Anka ya shaidawa Legit Hausa cewa idan aka ɗauki matakai cikin hanzari, za a gyara muhalli kuma ɗumamar yanayi da ake fuskanta zai ragu.

Kara karanta wannan

"Makaho ne kaɗai zai ce Tinubu ya gaza" Minista ya maida zazzafan martani ga NEF

Shuka bishiyoyi zai taimaka wajen gayara muhalli
A cewar Anka, ana buƙatar bishiya akalla daya tsakanin gidaje biyar don yaƙar dumamar yanayi Hoto: Getty images
Asali: Getty Images

A kalamansa:

"Duniya ba ta kai wannan gaɓar da za a ce ta kai yadda ba za a iya dawowa baya ba, duk da cewa muna da yawa."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun a farkon shekarar nan ne hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NIMET) ta yi gargadin za a fuskanci matsanancin zafi a wasu johohin Arewa kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Jihohin da ta ce na fuskantar barazanar tsananin zafi sun haɗa da Abuja, Kano, Sokoto, da jihar Kogi kamar yadda Premium Times Nigeria ta wallafa.

Dasa Bishiya 1 Tsakanin Gidage 5

A cewar mai fafutukar kare Muhalli, Umar Saleh Anka, akwai buƙatar a jerin kowane gida biyar, a samu aƙalla bishiya guda ɗaya. Anka ya ce ana yawan gine-gine, ana yawan hawa babura da sauran abubuwan hawa, kuma duk yawancin gidajen da ake ginawa sababbi ba a dasa bishiyoyi gaskiya a ciki.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya kawo mafita ga yan Najeriya kan ƙoƙarin Tinubu na kawar da ƴan bindiga

Mai fafutukar kare muhallin ya ce akai bambanci sosai tsakanin iskar wurin da ake da bishiya da wurin da babu. "Ya kamata a ce duk gida biyar, akwai bishiya misali guda ɗaya a kusa da ita, a iya ɗaukan ta ma a matsayin bishiyar al'umma."

"Za a yi tsananin zafi," NIMET

Hukumar NIMET ta yi gargaɗin za a fuskanci tsananin zafi a jihohin Borno da Yobe yayin bukukuwan sallah ƙarama.

Amma a wasu jihohin kamar Kebbi, tsawa za ayi na kwanaki uku, wato daga Litinin zuwa Laraba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel